Sanatoci Sun Amince da Hukuncin Kisa Kan Masu Safarar Kwayoyi, an Samu Hatsaniya

Sanatoci Sun Amince da Hukuncin Kisa Kan Masu Safarar Kwayoyi, an Samu Hatsaniya

  • Yayin da matsalar safarar kwayoyi ya yi katutu a Najeriya, Majalisar Dattawa ta dauki mataki kan lamarin
  • Majalisar ta amince da hukuncin kisa kan duk wanda aka kama da safarar kwayoyi ko samar su da kuma rarraba su ga al'umma
  • Wannan ya biyo bayan gabatar da rahoton kwamitin 'yancin dan Adam da kuma NDLEA karkashin jagorancin, Sanata Mohammed Monguno

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Majalisar Dattawa ta amince da hukuncin kisa kan wadanda aka kama da safarar kwayoyi.

Majalisar ta tabbatar da wannan doka a yau Alhamis 9 ga watan Mayu yayin zamanta a birnin Abuja.

Majalisar Dattawa ta ɗauki mataki kan masu safarar kwayoyi
Majalisar Dattawa ta amince da hukuncin kisa kan masu safarar kwayoyi. Hoto: The Nigerian Senate.
Asali: Facebook

Musabbabin daukar mataki kan safarar kwayoyi

Kara karanta wannan

Majalisa ta amince da karin albashi ga wasu ma'aikata, an fadi yawan kuɗin

Wannan mataki ya biyo bayan gabatar da rahoto da kwamitin Majalisar a bangaren 'yancin dan Adam da fannin shari'a da kuma NDLEA.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban kwamitin Sanata Mohammed Monguno daga Borno ta Arewa shi ya gabatar da rahoton a gaban Majalisar, cewar Channels TV.

Dokar wacce ta tsallake karatu na uku za ta inganta ayyukan hukumar NDLEA da kuma sabunta muggan kwayoyi, The Nation ta tattaro.

Sashe na 11 na dokar a baya ya ce duk wanda aka kama da laifin safara da ajiya ko kuma samar da su zai fuskanci daurin rai da rai.

Safarar kwayoyi: Hukuncin kisa ko daurin rai

Dokar an sabunta ta zuwa mataki mai tsauri na hukuncin kisa kan dukkan wadanda aka kama da zargin laifuffukan da aka lissafo.

Duk da rahoton bai tabbatar da hukuncin kisa ba, Sanata Ali Ndume ya bukaci a sabunta daurin rai da rai din zuwa na kisa.

Kara karanta wannan

Majalisar wakilai ta umarci CBN ya dakatar da karbar harajin tsaron yanar gizo

Majalisa ta tabbatar da dokar kisa

Mataimakin shugaban Majalisar, Barau Jibrin ya tabbatar da dokar inda ya ce masu goyon bayan hakan sun yi rinjaye.

Sai dai Adams Oshiomole ya kalubalanci hukuncin inda ya ce wadanda ba su amince da hukuncin ba sun fi yawa.

Ya ce bai kamata abin da ya shafi rai da mutuwa ake gaggawa ba, sai dai Barau ya kalubalance shi da cewa ya yi latti inda aka karanto dokar karo na uku tare da tabbatar da ita.

Majalisa ta nemo hanyar dakile matsalar tsaro

Kun ji cewa Majalisar Wakilan Najeriya ta bukaci Bola Tinubu da ya dauko sojojin haya domin su taimaka wajen kawo karshen rashin tsaro.

Dan Majalisa mai wakiltar Chibok, Domboa da Gwoza a majalisar wakilai, Hon. Ahmed Jaha ne ya mika bukatar a gaban Majalisar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel