Gwamna Fubara Ya Dira Majalisa Yayin da Ake Batun Yunkurin Tsige Shi

Gwamna Fubara Ya Dira Majalisa Yayin da Ake Batun Yunkurin Tsige Shi

  • Gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara ya ziyarci majalisar dokokin jihar a daidai lokacin da rikicin siyasa ya sake kunno kai a jihar
  • Fubara ya ziyarci ɓangaren majalisar ne inda Martin Amaewhule da sauran ƴan majalisar da ke adawa da shi ke gudanar da zamansu na majalisa
  • Ziyarar Gwamna Fubara zuwa harabar majalisar ta zo ne sa’o’i 24 bayan da aka samu sabon ɓangare a majalisar wanda ya zaɓi sabon kakaki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Rivers - Gwamnan jihar Ribas, Siminalayi Fubara, ya ziyarci harabar majalisar dokokin jihar da ke birnin Port Harcourt a ranar Alhamis, 9 ga watan Mayu.

Ziyarar gwamnan na zuwa ne a daidai lokacin da ake batun ƴan majalisar sun fara shirya yunƙurin tsige shi.

Kara karanta wannan

Fubara vs Wike: An yi kira ga Bola Tinubu ya tsoma baki kan rikicin siyasar jihar Rivers

Fubara ya ziyarci majalisar dokokin Rivers
Gwamna Fubara ya ziyarci majalisar dokokin jihar Rivers Hoto: Sir Siminalayi Fubara
Asali: Facebook

Gwamna Fubara a majalisar Rivers

Tashar Channels tv ta sanya wani bidiyo wanda ya nuna lokacin da gwamnan ya isa harabar majalisar dokokin jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bidiyon ya nuna Mai girma Gwamna Simi Fubara tare da muƙarrabansa sun shiga cikin harabar majalisar dokokin jihar.

Meyasa Fubara ya kai ziyara majalisa?

Gwamnan yace ya je majalisar ne a matsayinsa na gwamnan jihar. Sai dai ya yi tattaki na tsawon mintuna uku a cikin harabar majalisar kafin ya tafi.

Ziyarar gwamnan ta zo ne a daidai lokacin da wani sabon rikici ya ɓarke a majalisar dokokin jihar.

Wasu daga cikin ƴan majalisar da ke biyayya ga Gwamna Fubara sun gana a ranar Laraba, 8 ga watan Mayu inda suka zaɓi Victor Oko-Jumbo, mamba mai wakiltar mazaɓar Bonny a matsayin kakakin majalisar.

An zaɓi sabon kakaki a majalisar Rivers

Kara karanta wannan

Sojoji sun dauki mataki bayan kwashe kwanaki a kauyen da aka kashe jami'ai

An zaɓi Victor Oko-Jumbo a matsayin sabon kakakin majalisar dokokin mai wakilai 32 da misalin ƙarfe 10:00 na safe yayin zaman majalisar na ranar Laraba, 8 ga watan Mayun 2024.

Sabon kakakin ya kasance ɗaya daga cikin ƴan majalisa huɗu da suka marawa gwamnan baya a farkon rikicin siyasar jihar Rivers.

A lokacin ne dai suka zaɓi Edison Ehie a matsayin kakakin majalisar amma daga baya ya yi murabus daga zama ɗan majalisar.

Daga baya Gwamna Fubara ya naɗa Edison Ehie a matsayin shugaban ma’aikatansa.

Batun tsige Gwamna Fubara

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙungiyar ƙananan hukumomin Najeriya (ALGON) reshen jihar Rivers, sun goyi bayan a tsige Gwamna Siminalayi Fubara na jihar.

Ƙungiyar ta kuma zargi gwamna da riƙe kuɗaɗen ƙananan hukumomin jihar waɗanda ya kamata su gudanar da ayyukansu da su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel