Majalisa Ta Amince da Karin Albashi Ga Wasu Ma'aikata, an Fadi Yawan Kuɗin

Majalisa Ta Amince da Karin Albashi Ga Wasu Ma'aikata, an Fadi Yawan Kuɗin

  • Majalisar Dattawa ta amince da kudirin karin albashi ga ma'aikatan shari'a a Najeriya yayin da ake cikin wani halin matsi
  • Kudirin da aka gabatar a gaban Majalisar ya tsallake karatu na biyu inda shugaban alkalai zai samu albashin N5.38m a wata
  • Sanata Ashiru Yisa daga jihar Kwara ne ya gabatar da kudirin a gaban Majalisar kan inganta albashi da alawus na ma'aikatan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Kudirin da ke neman karin albashi ga alkalai ya tsallake karatu na biyu a Majalisar Dattawa.

Majalisar ta sake karanto kudirin ne a yau Alhamis 9 ga watan Mayu yayin zamanta a birnin Tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

Sanatoci sun amince da hukuncin kisa kan masu safarar kwayoyi, an samu hatsaniya

Majalisa ta amince da karin albashi ga wasu ma'aikata
Kudirin karin albashi ga ma'aikatan shari'a a Majalisar Dattawa ya tsallake karatu na biyu. Hoto: The Nigerian Senate.
Asali: Facebook

Za a kara albashin alkalai a Najeriya

Wannan ya biyo bayan yunkurin sake duba karin albashin ma'aikatan shari'a da kuma alawus dinsu a fadin kasar, cewar The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanata Ashiru Yisa daga jihar Kwara wanda shi ne mataimakin shugaban masu rinjaye a Majalisar shi ya gabatar da kudiri, cewar Premium Times.

A ranar 20 fa watan Maris din wannan shekara, Majalisar Wakilai ta gabatar da kudiri domin ba shugaban alkalan Najeriya albashin N5.38m a wata.

Albashin da alkakai za su iya samu

Kudirin har ila yau, ya amince da biyan shugabannin kotunan koli N4.21m yayin da shugaban kotun daukaka kara zai samu N4.48m a wata.

Har ila yau, alkalan kotunan daukaka kara za su samu albashin N3.73n a kowane wata a Najeriya.

Alkalin babbar kotun Tarayya da alkalan manyan kotunan jihohi da kotunan Sharia da Kwastomari da sauransu za su samu N3.53m a wata.

Kara karanta wannan

N15tr: "Za mu binciki yadda aka ba da kwangilar titin Lagos-Calabar", Majalisa

Majalisa ta dauki mataki kan safarar kwayoyi

A wani labarin, mun kawo muku cewa Majalisar Dattawa ta amince da hukuncin kisa kan wadanda aka kama da safarar kwayoyi.

Majalisar ta tabbatar da wannan doka a yau Alhamis 9 ga watan Mayu yayin zamanta a birnin Abuja.

Wannan mataki ya biyo bayan gabatar da rahoto da kwamitin Majalisar a bangaren 'yancin dan Adam da fannin shari'a da kuma NDLEA.

Asali: Legit.ng

Online view pixel