Plateau: Ƴan Bindiga Sun Kashe Bayin Allah, Sun Tafka Mummunar Ɓarna a Arewa

Plateau: Ƴan Bindiga Sun Kashe Bayin Allah, Sun Tafka Mummunar Ɓarna a Arewa

  • Ƴan bindiga sun kai hari kauyen Kayarda, sun kashe mutum huɗu kuma sun jikkata wasu da dama a jihar Filato
  • Magajin garin ya bayyana cewa tun bayan harin mutanen garin suka shiga fargaba da zullumi saboda lamarin ya gigita su
  • Shugaban ƙaramar hukumar Qua’an Pan, Christopher Audu Manship, ya ce jami'an tsaro sun duƙufa da nufin kamo duk masu hannu a harin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Plateau - Wasu miyagun ƴan bindiga sun halaka mutum huɗu kuma sun ji wa wasu da dama raunuka a wani hari da suka kai a jihar Filato.

Kamar yadda The Nation ta ruwaito, ƴan bindigar sun aikata wannan ta'addanci ne a kauyen Kayarda da ke yankin Namu ranar Talata da ta gabata da daddare.

Kara karanta wannan

Dubu ta cika: An kama 'yan canji 17 a kasuwar musayar kuɗi a jihar Kano

Gwamna Mutfwang na jihar Filato.
'Yan bindiga sun shiga kauye da daddare, sun yi ajalin mutum 4 a jihar Filato Hoto: Celeb Mutfwang
Asali: Facebook

Shugaban kwamitin rikon kwarya na ƙaramar hukumar Qua’an Pan watau kantoma, Christopher Audu Manship, ya tabbatar da faruwar lamarin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya kuma ziyarci waɗanda harin ya shafa tare da rakiyar manyan jami'an ƙaramar hukumar da kuma shugabannin tsaron yankin.

Wane mataki hukumomin Plateau suka ɗauka?

Mista Manship ya tabbatarwa mazauna yankin cewa tuni hukumomin tsaro suka fara aiki ba ji ba gani domim bankaɗo duk wanda ke da hannu a lamarin.

Ya jaddada cewa gwamnatinsa ba za ta bari wasu ɓata gari su kara wa al'umma ciwo da wahala ba duk da halin da ake fama da shi na ƙuncin rayuwa.

Magajin garin kauyen Kayarda ya ce har yanzu al’ummarsa na cikin kaduwa da alhinin abin da ya faru.

Ƴan bindiga sun miƙa wuya a Plateau

Wannan hari na zuwa ne sama da makonni biyu bayan wasu gungun ƴan bindiga sun tuba sun miƙa wuya a ƙaramar hukumar Wase da ke jihar Filato.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun hallaka mutum 8 tare da sace manajan banki a Zamfara

Gwamnatin jihar ƙarƙashin jagorancin Gwamna Celeb Mutfwang ta sanar da cewa ƴan bindigar sun miƙa bindigu ƙirar AK-47 ga hukumomi.

A cewar gwamnatin, ƴan bindigar sun amince sun ajiye makamansu ne bayan doguwar tattauna wa da wakilan gwamnatin Filato, rahoton Daily Trust.

An kashe sojoji 21 a Anambra?

A wani rahoton na daban, rundunar ƴan sanda ta musanta rahoton da ake yaɗawa cewa an yi wa sojoji 21 kisan gilla a Onitsha ta jihar Anambra.

Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar ƴan sandan jihar, Tochukwu Ikenga, ya yi kira ga ɗaukacin al'umma su yi watsi da ƙagaggen labarin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel