Latest
Masarautar Bichi ta yabawa Shugaba Bola Tinubu da kuma kokarin jami'an tsaro da bangaren shari'a wurin tabbatar da zaman lafiya a Kano yayin da ake cikin wani hali.
Gwamnatin jihar Edo karkashin jagorancin Gwamna Godwin Obaseki ta fara biyan sabon mafi karancin albashi na N70,000 ga ma'aikata a jihar mai arzikin man fetur.
Wata kungiyar Arewa, 'Arewa Social Contract Initiative' ta roki Sarki Aminu Bayero (da aka tube) da ya bar jihar Kano yanzu domin a samu zaman lafiya a jihar.
'Dan majalisar ttarayya, Alex Ifeanyi Mascot Ikwechegh ya bar addinin da yake yi, ya zama musulmi kamar yadda wani ya yada a dandalin sada zumunta a karshen mako.
Kungiyar SERAP ta bukaci Shugaba Bola Tinubu da ya yi amfani da bikin cika shekara daya a kan karagar mulki wajen bayyana yawan kadarorin da ya mallaka.
Rundunar 'yan sanda a jihar Kogi da ke Arewacin Najeriya ta sanar da cewa ƴan bindiga sun yi ajalin daliban Jami'ar jihar da suka sace a farkon wannan wata.
Wani masallaci ya rufto kan masallata a jihar Legas. Ana fargabar cewa mutane da dama ne da ke Sallah a cikin masallacin suka rasa rayukansu bayan aukuwar lamarin.
Gwamnatin tarayya ta shigar da kara a gaban Kotun Koli a kan gwamnonin jihohin kasar nan 36 a kan zargin rashin da’a yayin gudanar da kananan hukumomi.
Jami'an tsaro sun dauki matakin kulle hanyar da ke zuwa fadar da Alhaji Aminu Ado Bayero yake zaune a Kano. Hakan na zuwa ne yayin da ake takaddama kan sarautar Kano
Masu zafi
Samu kari