Lokaci Ya Yi da Tinubu Zai Bayyanawa ’Yan Najeriya Yawan Dukiyar da Ya Malaka, in Ji SERAP

Lokaci Ya Yi da Tinubu Zai Bayyanawa ’Yan Najeriya Yawan Dukiyar da Ya Malaka, in Ji SERAP

  • An nemi Shugaba Bola Tinubu da ya wallafa bayanan kadarorin da ya mallaka a yayin da ya cika shekara daya a kan karagar mulki
  • Kungiyar SERAP wadda ta gabatar da bukatar ta kuma nemi Kashim Shettima, ministoci, da gwamnoni su ma su bayyana kadarorinsu
  • SERAP ta kuma nemi Tinubu da ya samar da manhajar da jami'an gwamnati za su rika bayyana kadarorinsu kafin da bayan yin aiki

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Kungiyar kare hakkokin tattalin arziki da tabbatar da bin diddigi (SERAP) ta bukaci Shugaba Bola Tinubu da ya gaggauta wallafa bayanan kadarorin da ya mallaka.

SERAP ta gabatar da bukatu ga Tinubu
SERAP ta nemi Tinubu da gwamnoni su wallafa bayanan kadarorin da suka mallaka. Hoto: @officialABAT
Asali: Twitter

SERAP ta nemi sanin yawan dukiyar Tinubu

Kara karanta wannan

Ministar Tinubu ta ji wuta, ta ba da tulin kyaututtuka ga ƴan mata 100 da za a aurar

SERAP ta bukaci Tinubu da ya yi amfani da bikin cika shekara daya a kan karagar mulki domin ya nuna wa 'yan Najeriya gaskiyarsa da kuma tabbatar da dimokuradiyya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jaridar Daily Trust ta kuma ruwaito SERAP ta bukaci Tinubu da ya ka karfafi guiwar Kashim Shettima, ministoci, da gwamnonin jihohi domin su ma su bayyana kadarorin su.

SERAP ta jaddada bukatar ta ga Tinubu na:

"Yin gyaran fuska ga kundin tsarin mulki da zai haɗa da tanadin samar da manhajar da jami'an gwamnati za su rika bayyana kadarorinsu kafin da kuma bayan yin aiki a ma’aikatun gwamnati.”

Manufar Tinubu ya bayyana dukiyarsa

Rahoton Channels TV ya nuna mataimakin daraktan SERAP, Kolawole Oluwadare ne ya gabatar da bukatar a cikin wata budaddiyar wasika da ya fitar a ranar 25 ga Mayu 2024.

Kara karanta wannan

Tinubu zai kaddamar da jirgin kasan Abuja, ya yi albishir 1 ga yan Najeriya

“Wallafa bayanan kadarorin da ka mallaka da kuma ƙarfafa guiwar mataimakin shugaban kasa, ministoci, da gwamnonin jihohi su ma su yi hakan zai kara jawo yardar al'umma a kanku.
“Fadin gaskiya yayin bayyana kadarorin manyan jami’an gwamnati zai karfafa dimokuradiyyar kasar nan da kuma samar da rikon amana a dukkan matakan gwamnati."

- A cewar Kolawole Oluwadare.

Gwamnati ta maka gwamnoni a kotu

A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnatin tarayya ta maka gwamnonin Najeriya 36 a gaban Kotun Koli kan batutuwan da suka shafi kananan hukumomi.

Yayin da gwamnatin ke rokon kotun ta ba kananan hukumomin cikakken 'yancin cin gashin kai, ta kuma nemi da a hana gwamnoni kafa kwamitocin rikon kwarya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.