Gwamna Ya Cika Alkawari Ya Fara Biyan Sabon Mafi Karancin Albashi a Jiharsa

Gwamna Ya Cika Alkawari Ya Fara Biyan Sabon Mafi Karancin Albashi a Jiharsa

  • Gwamnatin jihar Edo ƙarƙashin ta fara biyan ma'aikata sabon mafi ƙarancin albashi na N70,000 a duk faɗin jihar
  • Gwamna Godwin Obaseki a kwanakin baya ne dai ya yi alƙawarin ƙara mafi ƙarancin albashin ma'aikatan jihar zuwa N70,000
  • Gwamnatin jihar ta fara biyan sabon mafi ƙarancin albashin na N70,000 a wannan watan na Mayun 2024

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Edo - Gwamnatin jihar Edo ta fara biyan sabon mafi ƙarancin albashi na N70,000 ga ma’aikata a jihar.

Hakan dai cika alƙawarin da gwamnan jihar Godwin Obaseki ya ɗauka ne na ƙara mafi ƙarancin albashin daga watan Mayun 2024.

Gwamnan Edo ya fara biyan sabon mafi karancin albashi
Gwamna Godwin Obaseki ya fara biyan ma'aikata sabon mafi karancin albashi Hoto: Godwin Obaseki
Asali: Facebook

A kwanakin baya ne dai yayin ƙaddamar da sabon ofishin ƙungiyar ƙwadago na jihar, Gwamna Godwin Obaseki ya sanar da ƙara mafi ƙarancin albashin ma’aikata a jihar daga N40,000 zuwa N70,000.

Kara karanta wannan

Sarkin Kano: Matasan Arewa sun rubuta wasika ga Tinubu, sun yi muhimmin gargadi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Obaseki ya biya mafi ƙarancin albashi

A wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labarai da wayar da kan jama’a na jihar, Chris Nehikhare, ya fitar a ranar Lahadi, ya ce an fara biyan mafi ƙarancin albashin ne a albashin watan Mayu, cewar rahoton jaridar Vanguard.

Kwamishinan ya ce biyan mafi ƙarancin albashin na N70,000 ya ƙara nuna irin jajircewar da Gwamna Obaseki yake yi domin kyautata jin daɗin ma’aikatan jihar Edo, rahoton jaridar The Punch ya tabbatar.

"Gwamnatin jihar Edo ta biya albashin ma’aikata a jihar na watan Mayu, wanda ya ƙunshi aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashi na N70,000."
"Wannan ya kasance cika alƙawarin da Gwamna Godwin Obaseki ya yi na ƙara mafi ƙarancin albashi daga N40,000 zuwa N70,000 daga wannan watan, a wani ɓangare na rage raɗaɗin taɓarɓarewar tattalin arziƙi."

- Chris Nehikhare

Kara karanta wannan

Gwamna Radda ya kawo hanyar magance rashin tsaro a Najeriya

Kwamishinan ya buƙaci ma’aikata da su jajirce wajen gudanar da ayyukansu, tare da bayar da gudummawa yadda ya kamata domin tabbatar da cewa gwamnan ya kammala wa'adinsa cikin jin daɗi.

Wata miyar sai a makwabta

Legit Hausa ta tuntuɓi wani ma'aikacin gwamnati a jihar Katsina, wanda ya yi fatan cewa ya kamata gwamnatin jihar ta waiwaye su kan ƙarin albashi.

Ya bayyana cewa ƙarin albashin zai taimaka wajen rage raɗaɗi ga ma'aikata duba da yadda rayuwa ta yi tsada a halin yanzu.

Ya bayyana cewa:

"Gaskiya ya kamata gwamnati ta waiwayi ma'aikata kan batun ƙarin albashi ko sun samu sauƙi kan halin matsin da ake ciki a halin yanzu."

Ma'aikata na son a biya N850,000

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙungiyoyin ƙwadago na NLC da TUC sun buƙaci a biya ma’aikatan jihar Akwa Ibom N850,000 a matsayin mafi karancin albashi.

Shugaban kungiyar NLC na jihar, Kwamared Sunny James ne ya bayyana haka yayin taron jin ra’ayin jama’a da gwamnatin tarayya ta shirya kan mafi ƙarancin albashi a garin Uyo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel