APC Za Ta Karbe Kudu Maso Gabas Idan Na Zama Gwamna, in Ji Chukwuma

APC Za Ta Karbe Kudu Maso Gabas Idan Na Zama Gwamna, in Ji Chukwuma

  • Mai neman takarar kujerar gwamnan jihar Anambra karkashin jam’iyyar APC, Paul Chukwuma ya yi magana kan muradunsa na takara
  • Paul Chukwuma ya ya sha alwashin cewa gaba daya jihohin Kudu maso Gabas za su dawo karkashin APC idan ya zama gwamna
  • A cikin shirinsa na ganin nasarar APC, Chukwuma ya dauki hayar ofisoshin yakin zaben jam'iyyar a dukkanin mazabun jihar

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Anambra - Tsohon mai binciken APC na kasa, Paul Chukwuma ya sha alwashin cewa gaba daya jihohin Kudu maso Gabas za su dawo karkashin jam’iyyar idan ya zama gwamnan Anambra.

Abin da Paul Chukwuma kan takarar gwamnan jihar Anambra
Paul Chukwuma ya bayyana manufofinsa kan zama gwamnan jihar Anambra a 2025. Hoto: Sir Paul Chukwuma, CeeCeeSoludo
Asali: Facebook

Chukwuma ya fara kokarin takarar gwamna

Kara karanta wannan

Kotu ta raba gardama kan sahihancin zaben gwamnan APC, ta jero hujjoji

Ya kuma yi alkawarin cewa nasarar da jam’iyyar za ta samu a zaben gwamnan jihar Anambra da ke tafe a 2025, zai zama wata babbar alama ta mamaye shiyyar a zabuka masu zuwa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin shirinsa na ganin nasarar jam’iyyar, ya ce ya dauki haya tare da bayar da gudummawar ofisoshin yakin zaben APC a dukkanin mazabun jihar, in ji rahoton Leadership.

An ce Chukwuma ya mika makullan ofisoshin jam’iyyar ga mambobin kwamitin gudanarwa na jam’iyyar na jiha karkashin jagorancin shugaban jam’iyyar, Cif Basil Ejidike.

Chukwuma zai kara da Gwamna Soludo

Sir Paul Chukwuma, ya ce zai kayar da gwamnan jihar Anambra mai ci, Farfesa Charles Soludo idan ya lashe tikitin takarar gwamna na jam'iyyar APC a 2025.

Jaridar The Sun ta ruwaito dan siyasar yce zai rika shirya tarukan karawa juna sani a tsakanin shugabannin jam'iyyar a dukkan matakai na jihar.

Kara karanta wannan

Jami'an DSS sun mamaye fadar Sarkin Kano? Gaskiyar abin da ya faru ta bayyana

Ya bayyana kudurinsa na baiwa jam’iyyar APC gagarumin goyon baya, tallafin kudi, da kwarin guiwa domin yin zarra a tsakanin jam’iyyun siyasa na jihar.

Gwamnatin tarayya ta yi karar gwamnoni

A wani labarin, mun ruwaito gwamnatin tarayya ta yi karar gwamnoni 36 na jihohin Najeriya a Kotun Koli domin nemawa kananan hukumomi 'yancin cin gashin kansu.

Babban lauyan tarayya (AGF) kuma ministan shari’a ne ya shigar da karar karar mai lamba SC/CV/343/2024 a ranar 20 ga Mayu a madadin gwamnatin tarayya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel