Matashi dan Najeriyan da ya auri baturiya sa'ar mahaifiyarsa ya rabu da ita

Matashi dan Najeriyan da ya auri baturiya sa'ar mahaifiyarsa ya rabu da ita

- Usman Umar ya caccaki tsohuwar matarsa, Lisa Hamme, bayan aurensu ya mutu

- Mawakin dan Najeriya ya daura bidiyon daurin aurensu inda yake godewa Allah da ya ceceshi

- Umar ya auri Lisa wacce ta girmesa da shekaru 23 duk da fadace-fadacen da sukeyi yayin soyayya

- Masoyan biyu sun soki juna yayinda suka rabu

Mawaki dan Najeriya, Usman Umar, wanda akafi sani da Soja Boy, ya jefa abin magana cikin jama'a yayinda ya caccaki tsohuwar matarsa, Lisa Hamme.

A bidiyon da ya daura a shafinsa na Instagram, Soja Boy ya bayyana yadda ya rabu da ita kuma yana godewa Allah da ya 'yantar da shi daga hannunta.

Ya bayyana yadda mahaifiyarsa ta nuna rashin jin dadinda da auren mace sa'arta wacce ta girmeshi da shekaru 23.

Usman ya godewa Allah kuma yace da alamun asiri tayi masa.

Yace: "Ko dai an yaudarni ko kuma an yi mi asiri, kalli fuskar mahaifiyata da dan'uwana, gaba daya basu ji dadi ba amma a haka na cigaba. Na godewa mai sama da ya 'yantar da ni."

Matashi dan Najeriyan da ya auri baturiya sa'ar mahaifiyarsa ya rabu da ita
Matashi dan Najeriyan da ya auri baturiya sa'ar mahaifiyarsa ya rabu da ita Hoto: Instagram/officialsojaboy
Asali: Instagram

Kalli jawabin da yayi:

KU KARANTA: Kada ku dogara da gwamnati don samun aiki, Ministan Buhari

A wani labarin mai alaka, an daura auren matashi dan asalin jihar Kano, Suleiman Isah, da amaryarsa baturiyar kasar Amurka, Jenine Anne Reimann, a yau, Lahadi, a wani masallaci da ke cikin barikin 'yan sanda a unguwar Panshekara Kano.

Dandazon mutane ne suka halarci wurin taron daurin auren inda suka taya ma’auratan murna.

Mahaifin ango da abokansa sun halarci daurin aure kuma sun bayyana farin cikinsu da jin dadi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng