Jarumar Kannywood, Bilkisu Ta Saki Sababbin Hotuna da Suka Bayyana Surar Jikinta
- Jarumar Kannywood Bilkisu Salis ta gamu da fushin mutane kan shigar da ta yi a wasu sababbin hotuna da ta saki kwanan nan
- Masu bibiyar jaruma Bilkisu sun yi tsokaci iri-iri, wasu na yabawa kyawunta, yayin da wasu da dama ke caccakar shigar da ta yi
- Sama da mutane 1,100 sun nuna alamar kauna ga hotunan, yayin da wasu masu tsokaci ke jan hankalinta kan bin dokokin addini
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kano - Wata 'yar wasar Kannywood, Bilkisu Salis, ta saki wasu sababbin zafafan hotuna a shafukan sada zumunta da suka jawo mata zagi.
Masoya da masu bibiyar jarumar a soshiyal midiya sun nuna matukar bacin ransu kan "mummunar" shigar da ta yi kuma ta wallafa a yanar gizo.

Asali: Instagram
A ranar Juma'a, jaruma Bilkisu Salis ta wallafa hotunan da ake ta ka-ce-na-ce a kansu a shafinta na Instagram mai mabiya sama da 66,000.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A yayin da ta wallafa hotunan, 'yar wasar kwaikwayon ta yi addu'o'i da Larabci tana mai cewa:
"Ya Ubangiji ka sanya ni da zuriyata mu zamo masu tsayar da Sallah. Ya Ubangiji ka karɓi addu'ata.
"Ya Ubangiji ka gafarta mini, da iyayena da dukkan muminai a ranar da za a tsayar da hisabi."
Sama da mutane 1,100 suka nuna alamar 'kauna' a kan hotunan da ta wallafa, yayin da sama da mutane 50 suka tofa albarkacin bakinsu.
Mutane sun yiwa jaruma Bilkisu tatas
A yayin da wasu daga cikin masu tsokaci suka rika kuranta kyawun jarumar, wasu a hannu daya sun yiwa Bilkisu tatas kan irin shigar da ta yi.
A zantawarmu da Amina Lawal, ta ce abin takaici ne yadda jaruman masana'antar Kannywood ke ado da tsiraici duk da kiraye kirayen da mutane suke yi.
Amina Lawal ta ce:
"Nakan gaza gane dabarar wasu matan Kannywood na nuna tsiraicinsu a bidiyo ko a hotunan da suka dorawa a shafukansu na sada zumunta.
"Ire iren wadannan shigar da jaruman ke yi ce ke sawa jama'a su rika aibata masana'antar Kannywood, tare da yiwa jaruman lamba da masu yawan 'ta zubar.'"
Sai dai Amina Lawal ta ce ba dukkanin 'yan wasar Hausa mata ke irin wannan shiga ba, inda ta ce akwai jaruman da kowa ya shaida suna shigar mutunci.
"Jarumai irinsu Hadiza Gabon, Jamila Nagudu, Aisha Aliyu Tsamiya duk da ta yi aure na daga cikin masu mutunta kansu ta hanyar yin shiga mai kyau."
- A cewar Amina Lawal.
Legit Hausa ta tattaro kadan daga ra'ayoyin masu bibiyar jarumar kan hotunan da ta wallafa:
realharunzender:
"Masha Allah, da kyau da kyau, fatan nasara jarumata."
huzzy_boy_:
"Wallahi a ji tsoron Allah."
dannazi014:
"Allah ya shirya ki, amma avacoin dinki duk a waje, wata rana uwa ce ke."
queen_fiddau13:
"Ba za dai ki bari ba, duk da wa'azantuwar da mutuwa ke mana."
real_sulee2000:
"Nonuwanki a waje, Allah ya kyauta."
shariff_mahmud_
"Ke da nake girmamawa za ki yi wannan shigar? Wallahi Annabi ya tsinewa wannan shigar."
realnasirabdullahi:
"kofar aljanna a bude take, kofar wuta ma a bude take sai wadda ka ga damar shiga."
abbasgas1:
"Kin yi kyau, amma gaskiya kin bar nonuwanki a waje."
saifullahisabowaizi:
"Bai dace da ke ba irin wannan shigar, haramun ne, ya kamata ki hankalta. Akwai mutuwa tana zuwa kowane lokaci."
Kalli hotunan jarumar da suka tayar da kura a kasa:
Hotuna: Jaruma Rayya ta jawowa kanta magana
A wani labarin, mun ruwaito cewa ma'abota soshiyal midiya sun yiwa jarumar Kannywood, Rayya Kwana Casa'in kaca kaca kan shigar da ta yi.
A wasu hotuna na murnar karin shekara da Rayya ta fitar, an ga jarumar ta yi shigar da ta nuna wasu sassan jikinta, lamarin da ya jawo ce-ce-ku-ce.
Asali: Legit.ng