Bayan Rahama Sadau, Wata Jarumar Fina Finai Ta Sake Samun Mukami a Abuja

Bayan Rahama Sadau, Wata Jarumar Fina Finai Ta Sake Samun Mukami a Abuja

  • Kakakin Majalisar Wakilan tarayya, Tajudden Abbas ya naɗa jarumar fina-finan Nollywood mukami a ofishinsa
  • Rt. Hon. Tajuddeen Abbas ya ba Eniola Badmus muƙamin hadimansa a bangaren harkokin al'umma da tsare-tsare
  • Badmus tana daya daga cikin jarumai da suka ba da gudunmawa da goyon bayan jam'iyyar APC a zaben da ya wuce

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Jarumar fina-finan Nollywood, Eniola Badmus ta samu muƙami daga kakakin Majalisar Wakilai, Tajudden Abbas.

Abbas ya naɗa Badmus Eniola a matsayin hadima ta musamman kan korafin al'umma da tsare-tsare da kuma bukukuwa.

Jarumar fina-finai ta samu mukami a Abuja bayan Rahama Sadau
Jarumar Nollywood, Eniola Badmus ta samu babban mukami makwanni kadan bayan ba Rahama Sadau. Hoto: @eniolabadmus/@tajudeenabass.
Asali: Instagram

Goyon baya da jarumar ta ba APC

Nadin jarumar ya bayyana ne a yau Juma'a 10 ga watan Mayu bayan yada shi a kafofin sadarwa, cewar Tribune.

Kara karanta wannan

"Yana da kyau amma...": Dattawan Arewa sun bayyana matsayarsu kan harajin CBN

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jarumar ta yi kaurin suna wurin nuna goyon bayanta ga jam'iyyar APC duk da irin kushewa da caccakar da ta sha a wurin jama'a.

Sai dai wannan nadin na jarumar ya jawo kace-nace a tsakanin al'ummar Najeriya, PM News ta ruwaito.

Wasu jama'a da dama sun taya ta murnan samun wannan mukami yayin da wasu ke kushewa.

Martanin mutane kan nadin Badmus

@TaoFeek182:

"Wannan nadin ya dace da ke, na miki murna, kin dage wurin tabbatar da kasancewa cikin jam'iyyar kafin da kuma bayan zabe, bai kamata a manta da ke ba."

@Alpha_Femalee:

"Yanzu na gane meyasa ta dage a zaben da aka gudanar, na miki murna da samun hadima ga kakakin Majalisar Wakilai, Tajudden Abbas."

@BlummyZusi:

"Badmus ta samu abin da ta ke nema tuntuni, amma ai zasu gina mata ofis saboda ban gane irin wannan mukami ba."

Kara karanta wannan

'Yan bindiga: Majalisa ta bukaci samar da jami'an tsaron hadin gwiwa a Niger

Rahama Sadau ta samu muƙami

A wani labarin, an ji Gwamnatin Tarayya ta nada jarumar fina-finai Rahama Sadau a matsayin mamba a kwamitin gwamnati da ke kula da shirin saka hannun jari .

Rahotanni sun bayyana cewa mataimakin shugaban kasa Kashim Ibrahim Shettima ne ya kaddamar da kwamitin a Abuja.

Shirin iDICE hadin guiwa ne tsakanin gwamnati da hukumomin duniya da suka hada da bankin masana'antu da bankin raya Afrika.

Asali: Legit.ng

Online view pixel