Allah Ka Cece Mu: Hoton Jarumar Fim Tare Da Tinubu Ya Yi Fice, Yan Najeriya Sun Yi Martani

Allah Ka Cece Mu: Hoton Jarumar Fim Tare Da Tinubu Ya Yi Fice, Yan Najeriya Sun Yi Martani

  • Wani hoto da jarumar fim Eniola Badumus ta wallafa a soshiyal midiya na ubangidanta dan takarar shugaban kasa na APC, Bola Tinubu ya yadu
  • Eniola Badmus wacce ke yawan shan suka tun bayan da a fito ta ayyana goyon bayanta ga Asiwaju ta sake shan caccaka a kan hotonta da na Jagaban
  • Mutane sun bayyana hoton wanda a yanzu ta goge a Instagram a matsayin mai ban dariya

Shahararriyar jarumar Nollywood kuma mamba a jam'iyyar All Progressive Congress (APC) mai mulki, Eniola Badmus ta haddasa cece-kuce a soshiyal midiya bayan ta wallafa wani hoton ubangidanta.

A hoton da Eniola Badmus ta wallafa a Instagram wanda a yanzu ta goge shi, an gano dan takarar shugaban kasar na jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu zaune cikin wani yanayi.

Kara karanta wannan

2023: A Karshe Atiku Ya Magantu A Kan Fallasar Da Tsohon Hadiminsa Ya Yi Masa Kan Zargin Wawure Kudi

Eniola Badmus da Bola Tinubu
Allah Ka Cece Mu: Hoton Jarumar Fim Tare Da Tinubu Ya Yi Fice, Yan Najeriya Sun Yi Martani Hoto: eniola_badmus
Asali: Instagram

Yan Najeriya sun yi martani ga hoton, inda wasu suka tambayi Eniola Badmus dalilinta na wallafa irin wannan hoto na ubangidanta. Yayin da wasu suka yi wa dan ta'karar na APC da jarumar ba'a, wasu sun fara neman suna da shi.

Kalli wallafar jarumar da ya haddasa cece kuce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jama'a sun yi martani

@thedonperry687:

"Bayan zabe za ku ji ta siya gida a lekki da sabuwar motar G Wagon ku ci gaba da wasa ita kuma tana kama kudi."

@iamtreasurenla:

"Me yasa kika goge hoton shugaban kasar ki ba kya alfahari da wanda kike yi wa kamfen ne maciya amana."

@beethicks:

"Baki dai isa ki goge wannan kwafin hoton daga wayata ba."

@aadexinteriors:

"Da sai ta fada ma baba ya rufe bakin saboda kuda."

@colnight:

Kara karanta wannan

Wahalar Naira Da Mai: Akwai Wasu Na Kusa Da Buhari Da Basu Son Tinubu Yaci Zabe, El-Rufa'i

"Bata boye ba! Tana goyon bayan APC fili, ku kyale mutane su yi abunsu."

@emryzlawd:

"Yanzu na ga dalilin da yasa davido ya daina binki."

@blaqson_of_lagos:

"Hulan ne ya bani dariya. Baba ya yi kamar wani maye."

@king_oladway:

"Ki ci gaba da sha'aninki Eniola, dukkanku ba za ku iya caccakar Akindele Funke don ta goyi bayan Atiku ba, amma kun bude kanku mara tunani don caccaka da muzanta Eniola Badmus. Ba ku da hankali ko."

A wani labari na daban, mun ji cewa matar shugaban kasa, Aisha Buhari, ta goyi bayan ikirarin da gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya yi na cewar akwai wasu na kusa da fadar shugaban kasa da basa so Bola Tinubu ya ci zabe a 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel