An Yankewa Ɗan Kasuwa Hukuncin Ɗaurin Wata 6 a Gidan Yari Saboda Laifin Damfarar Mai Sana'ar Tumatur

An Yankewa Ɗan Kasuwa Hukuncin Ɗaurin Wata 6 a Gidan Yari Saboda Laifin Damfarar Mai Sana'ar Tumatur

  • Wata kotun majistare da ke zamanta a Jos, babban birnin jihar Filato ta yankewa Abubakar Usman, ɗan kasuwar da ya damfari wani mai sana'ar tumatur
  • Kotun ta ce ta yanke ma Usman wannan hukuncin ne bisa samunsa da laifin zamba da cin amanar da aka ba shi
  • Mai shigar da ƙara ya ce mai siyar da tumaturin ya ba wa ɗan kasuwar kuɗi domin ya kawo masa kwanduna 20, amma daga nan sai ya sha shagalinsa da kuɗaɗen

Jos - Wata Kotun Majistare da ke Jos babban birnin jihar Filato ta yankewa wani ɗan kasuwa Abubakar Usman mai shekaru 28 hukuncin ɗaurin watanni shida a gidan yari.

Kotun, wacce ta yi zama yau Juma'a, ta yankewa Usman wannan hukunci ne bisa samunsa da laifin damfarar wani mai sayar da tumatir, in ji rahoton jaridar Punch.

Kara karanta wannan

Kotu Ta Soke Halascin Takarar Zababɓen Gwamna da Wasu 'Yan Takara a Jihohin Kano da Abiya

Kasuwar tumatur
Kotu ta yankewa dan kasuwa hukuncin wata shida a gidan yari bisa laifin damfara. Hoto: Punch
Asali: UGC

Hukuncin zai zama izina ga masu irin halinsa

Mai shari'a Shawomi Bokkos ce ta yankewa Usman hukuncin bayan ya amsa laifuka biyu da ake tuhumarsa da suka haɗa da cin amana, da kuma zamba cikin aminci.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Bokkos ta ce wannan hukuncin da aka yanke zai zama izina ga duk wasu masu shirin aikata irin hakan a gaba.

Sai dai kotun ta bai wa wanda ake tuhuma zaɓin biyan tarar kuɗi N10,000 maimakon zuwa gidan yarin.

Sannan ta kuma umarci wanda akai ƙarar da ya biya diyyar N50,000 ga wanda ya kai kara, wato ga mai sana'ar tumatir ɗin..

Dubu 50 aka ba shi domin ya kawo tumatur

Tun da farko dai jami'i mai shigar da ƙara, Ibrahim Gokwat, ya shaidawa kotun cewa an kai ƙarar ne a ranar 4 ga watan Mayu, a ofishin ‘yan sanda da ke Laranto ta hannun Anagor Ugo.

Kara karanta wannan

Babba Dalilin Da Yasa Gwamnan APC Ya Yi Shiru Kan Zargin da Ake Masa Na Wawure N70bn

Gokwat ya ce an bai wa wanda aka yankewa hukuncin N50,000 da zummar ya kawo kwanduna 20 na tumatir, amma sai kawai ya zuba kuɗaɗen aljihunsa ya sha sha'anin gabansa da su.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN), ya ce hukuncin wannan laifi dai na nan cikin kundin dokar Penal Code ta jihar Filato.

Wata mata ta ɗauki bidiyon 'yan damfara ba tare da sun sani ba

A wani labarin namu kuma, kun ji wata mata mai suna Stella da ta bayyana yadda ta shiga motar wasu 'yan damfara har sau biyu kuma ta yi sa'ar fitowa lafiya ba tare da ta rasa komai ba.

Matar ta ɗora wani bidiyo a shafinta na TikTok inda ta bayyana cewa ta haɗu da 'yan damfarar ne a mota, har ta yi musu bidiyo ba tare da sun ankara ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel