"Na So Yarana Su Yi Fim Amma Sun Nuna Ba Haka Ba", Jarumi Ali Nuhu

"Na So Yarana Su Yi Fim Amma Sun Nuna Ba Haka Ba", Jarumi Ali Nuhu

  • Shahararren jarumin masana'antar finafinai ta Kannywood, Ali Nuhu, ya bayyana abinda ya so ƴaƴan sa su zama
  • Ali Nuhu ya ce ya so ƴaƴan sa su zama manyan jarumai a harkar fim kamar sa, amma sai suka nuna ba haka ba
  • Kowanne daga cikin ƴaƴan ya zaɓi zama wani abu daban a rayuwa wanda ba harkar fim ba

Jihar Kano - Shahararren jarumi, mai shirya finafinai kuma mai bada umurni a masana'antar Kannywood, Ali Nuhu, ya bayyana cewa ya so ƴaƴan sa su yi harkar fim amma sai suka zaɓi bin wata hanyar daban.

Jaridar Daily Trust tace jarumi Ali Nuhu ya bayyana cewa, yaron sa Ahmad Ali Nuhu, wanda ya ke da shekara 16 a duniya, ya nuna yana son harkar tamola yayin ɗiyarsa Fatima, ta ke son karantar International relations a jami'a.

Kara karanta wannan

Majalisa ta 10: Kakaba Shugabannin Majalisar Wakilai Ya Kawo Rudani a APC, Wasu 'Yan Takara Sun Yi Bore

Ali Nuhu ya bayyana abinda ya so yayansa su zama
Jarumin masana'antar Kannywood, Ali Nuhu Hoto: RealAliNuhu
Asali: Instagram

Jarumin a wata hira da BBC Hausa, ya yi watsi da kalaman da ake jifar ƴan fim da su kan cewa, ba su son yin fim tare da ƴaƴan su.

A kalamansa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Maganar gaskiya na fi son ɗa na ya zama jarumi, amma ya nace cewa yana son zama ɗan ƙwallo. Don haka sai na goya masa baya, saboda a zamanin yanzu ba a takurawa ƴaƴa kan abinda kake so su zama."
"A matsayin mahaifi idan ka gano abinda yaran ka su ke sha'awar zama, sai ka goya mu su baya. Ni a karan kai na, na fi son mu yi fim tare amma sai ya nuna ɗan ƙwallon ƙafa ya ke son ya zama.
"Fatima ta nuna ba ta son fim lokacin tana da shekara 13 . Tana son karantar dangantaƙar ƙasa da ƙasa a jami'a, a yanzu haka ta kusa kammala 300L. Kuma Alhamdulillahi da goyon bayan da mu ke bata tana ɗaya daga cikin ɗalibai masu CGP babba a ajin su."

Kara karanta wannan

Akwai Matsala: Malamin Addini Ya Hango Gagarumar Matsala a Kawancen Tinubu Da Gwamnan PDP

Ali Nuhu Ya Janye Karar Da Ya Shigar Akan Hannatu Bashir

A baya mun kawo rahoto, kan yadda Ali Nuhu ya janye ƙarar da ya shigar da jarumar masana'antar finafinan Kannywood, Hannatu Bashir.

Ali Nuhu ya shigar da ƙarar ne akan jarumar saboda zargin ci masa mutunci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel