Maganar Aure Ta Yi Karfi Tsakanina Da Mustapha Waye Kafin Rasuwarsa, Hajara Izzar So

Maganar Aure Ta Yi Karfi Tsakanina Da Mustapha Waye Kafin Rasuwarsa, Hajara Izzar So

  • Aisha Babandi ta tabbatar da cewar akwai maganar aure tsakaninta da marigayi Mustapha Waye kafin rasuwarsa
  • Jarumar wacce aka fi sani da Hajara Izzar So ta ce ta shiga mawuyacin hali bayan samun labarin daraktan saboda shakuwar da ke tsakaninsu
  • Ta ce shine mutum na farko da ya daga darajarta har ta zama wata a rayuwa kasancewar ita marainiya ce ba uwa ba uba

Fitacciyar jarumar Kannywood, Aisha Babandi wacce aka fi sani da Hajara a cikin shirin ‘Izzar so’ mai dogon zango ta bayyana yadda ta shiga halin wayyo Allah bayan rasuwar babban darakta, Nura Mustapha Waye.

A wata hira da gidan radiyon Freedom na jihar Kano yayi da ita kuma Mujallar fim ta saurara, jaruma Aisha ta bayyana cewa sun shaku matuka da marigayin don har suna maganar yin aure a tsakaninsu

Mustapha Waye da Hajara Izzar So
Maganar Aure Ta Yi Karfi Tsakanina Da Mustapha Waye Kafin Rasuwarsa, Hajara Izzar So Hoto: aysha_bloody
Asali: Instagram

Kamar yadda Mujallar Fim ta rahoto, jarumar ta ce marigayin shine mutum na farko da ya taimake ta a rayuwa har ta kai ga zama wata domin dai ita din marainiya ce babu uwa babu uba.

Ta ce:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

“Dama chan muna tare kuma shine mutumin farko da ya taimaki rayuwata har na kai ga zama wata a rayuwa, kasancewar ni marainiyace bani da uwa, bani da uba kuma na tashi ne a gaban yayar mahaifiyata.”

Ta kuma bayyana cewa ko mutuwar iyayenta bata ji shi a jikinta kamar yadda ta ji na daraktan ba saboda dama chan ba a gabansu ta taso ba.

Ta kara da cewa:

“Kasancewar ban yi rayuwa tare da iyaye na ba ya sanya mutuwarsu bata taba ni kamar yadda mutuwar darakta Nura Mustapha Waye ta taba ni ba.

“Akwai soyayya da maganar aure a tsakaninmu kuma har abun ya yi karfi kafin Allah ya amshi ransa, saboda haka na shiga damuwa har ma ban san irin yadda zan kwatanta yadda na ji ba.”

Jarumar ta bayyana rashin a matsayin abin da ba za ta manta da shi ba inda tayi masa addu’ar Allah ya jikansa, ya bata makamancinsa.

Jaruma Halima Atete za ta amarce, an fara shagalin biki

A gefe guda mun kawo cewa an fara bikin auren shahararriyar jarumar fim, Halima Atete wacce za ta shiga daga ciki a ranar Asabar, 26 ga watan Nuwamba.

An fara shagalin bikin ne da wata yar liyafa wanda ya samu halartan amarya da yan uwa da abokan arziki, kuma amarya Halima ta fito shar da ita.

Asali: Legit.ng

Online view pixel