Matar Aure Ta Caki Mijinta Da Wuka Har Lahira Saboda Ya Nemi Hakkinsa

Matar Aure Ta Caki Mijinta Da Wuka Har Lahira Saboda Ya Nemi Hakkinsa

  • Wata matashiyar mata, Odunayo Olumale, ta shiga komadar yan sanda kan zarginta da ake da kashe mijinta ta hanyar daba masa wuka
  • Takaddama ta shiga tsakanin marigayin da matarsa ne bayan ya nemi ta basa hakkinsa na aure inda ita kuma ta nuna tirjiya
  • Kamar yadda rundunar yan sandan jihar Oyo ta bayyana, matar ta cakawa mijin nata wuka ne a kokarinta na martani ga fasa mata wayarta da marigayin yayi

Oyo - Wata matar aure mai shekaru 27 mai suna Odunayo Olumale ta soki mijinta mai suna Olamilekan Salahudeen da wuka har lahira saboda ya nemi ta bashi hakkinsa na aure.

Lamarin na zuwa ne a ranar da ma’auratan suka yi sulhu tare da kome a aurensu bayan watanni uku da rabuwa, jaridar The Nation ta rahoto.

Kara karanta wannan

Mutum 23 Sun Yanke jiki sun Fadi Yayin Tattakin Goyon Baya ga Tinubu da Shettima a Kano

Yan Sanda
Matar Aure Ta Caki Mijinta Da Wuka Har Lahira Saboda Ya Nemi Hakkinsa Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Ya Nemi ya hada gado da ita sai kokawa ya barke

Da yake jawabi a garin Ibadan yayin gurfanar da wacce ake zargin a hedkwatar rundunar yan sandan jihar Oyo, kakakin yan sandan, Adewale Osifeso, ya tabbatar da lamarin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kakakin yan sandan ya ce binciken farko ya nuna cewa marigayin da matarsa sun dawo gidansu da ke yankin Oko-Oba na Oyo a wannan ranar da abun ya faru bayan shafe watanni uku basa tare.

Osifeso ya ce:

“A ranar 17/11/2022 da misalin karfe 0350hrs, wani mutum mai suna Ismaila Tijani ya kai rahoto sashin yan sandan Dubar cewa da misalin 0223hrs of 16/11/2022, matar dansa Odunayi ta caki dansa mai suna Olamilekan Salahudeen da wuka.
“Marigayin ya yi yunkurin hada shimfida da matar tasa amma ta ki, lamarin ya kai ga har suka fara kokawa inda marigayin ya karbi wayan matar tasa sannan ya doka shi da kasa, a kokarin rama abun da yayi maa sai matar ta soke shi da wuka a kirjinsa, lamarin da yayi sanadin mutuwarsa.”

Kara karanta wannan

Kamar da wuya: Bidiyon yadda mata ta gwangwaje mijinta da kyautar mota Ferarri

Osifeso ya ce tuni wacce ake zargin ta amsa laifinta da kuma rawar da ta taka a mummunan lamarin, yana mai cewa za a mika a kotu da zaran an kammala bincike, rahoton Peoples Gazette.

Na rasa saurayi guduna maza suke yi saboda na kasance kurma, Budurwa ta koka

A wani labari na daban, wata kyakkaywar budurwa son kowa kin wanda ya rasa ta shiga damuwa saboda ta rasa wanda zai fito yace yana sonta.

Kamar yadda budurwar ta bayyana da zaran ta samu manemi sai ya ci na kare idan ya gano tana da nakasa, domin dai ita din kurma ce.

Asali: Legit.ng

Online view pixel