Kullun burinka ka zagi yan fim: Maryam Booth ta yi martani ga Naziru sarkin waka

Kullun burinka ka zagi yan fim: Maryam Booth ta yi martani ga Naziru sarkin waka

  • Jaruma Maryam Booth ta yi shagube ga Naziru Sarkin Waka kan kare iyayen da ke tura yayansu almajiranci
  • Maryam ta wallafa bidiyo inda wani malami ke magana kan iyayen da ke haihuwar ‘ya’ya alhalin basu da hanyar shigowar kudi
  • A martanin da jarumar ta yi, ta bayyana cewa tana jiran a bawa mallam amsa shima kamar yadda aka yiwa Nafisa Abdullahi

Shahararriyar jarumar Kannywood, Maryam Booth ta shiga sahun masu adawa da iyayen da ke tura yaransu wani waje da sunan almajiranci.

Sai dai Maryam ta yi shagube ne ga Naziru Sarkin Waka wanda ya fito ya caccaki masu adawa da tura yara almajiranci, harma ta kai ya kwancewa abokan sana’arsa zani kan haka.

Mawakin dai ya ce idan har ana neman wadanda iyayensu suka haife su amma suka kasa kula da su toh a tafi masana’antar fim.

Kara karanta wannan

Babu wacce iyayenta basu san yadda za su yi da ita ba sama da macen da za ta kama otel tana iskanci - Naziru

Kullun burinka ka zagi yan fim: Maryam Booth ta yi martani ga Naziru sarkin waka
Kullun burinka ka zagi yan fim: Maryam Booth ta yi martani ga Naziru sarkin waka Hoto: BBC Hausa
Asali: UGC

Da alama wannan furucin bai yiwa wasu daga cikin jaruman musamman mata dadi ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A wata wallafa da tayi a shafinta na Instagram, Booth ta saka bidiyon wani malami yana wa’azi a kan mutanen da ke haihuwar yara da yawa alhalin basu da hanyar shigowar kudi a duk wata don kula da su.

A kasan bidiyon, ta rubuta cewa tana jira abawa malamin amsa shima kamar yadda aka yiwa abokiyar sana’arta, Nafisa Abdullahi, wacce dama tun farko ita ce ta fara kalubalantar iyayen da ke tura yara almajiranci.

ta kuma bayyana cewa kafin su su fada malamai ne suka fara fadi amma shi Naziru kullun burinsa shine ya zagi yan fim.

Ta ce:

“Don Allah Ina jiran abawa malam answer shima. Ko dai dama mata kawai za ka iya mayarwa martani? Dan Allah ku tayani fassara masa don na tabbata yana bukatar haka.✌️”

Kara karanta wannan

Mai neman suna: Idan ka isa ka bugi kirji ka kira suna, Nafisa ga Sarkin Waka

Ta sake rubuta:

"Kafin mu fada malamai sun fada me yahana kabasu answer? Kullim burinka ka zagi yan film koma yaya ne ban zo da rigima ba ramadan kareem"

Jama'a sun yi martani

usman_nasirh ya ce:

"Xafa mu kara sakin video tamm"

ana_herleemerh ta yi martani

"Abin ai da rainin wayo, Sanusi Lamido ma yayi Alla-wadai da almajiranci amma har yau babu wanda ya kalubalance shi"

hannafi_dahiru_kagadama ya ce:

"Wanna magana haka yake Kanwata Ramadan Kareem"

Babu wacce iyayenta basu san yadda za su yi da ita ba sama da macen da za ta kama otel tana iskanci - Naziru

Mun kawo a baya cewa Naziru Sarkin waka ya sake yin zazzafan martani a kan furucin da jaruma Nafisa Abdullahi ta yi kan Almajirai da iyayensu.

Sarkin waka ya nuna bacin ransa, inda ya bayyana cewa babu wanda iyayensa suka yi asarar haihuwarsa sama da mutumin da zai sunga iskanci yana sakin hotuna duniya na zaginsa amma shi ko a jikinsa.

Kara karanta wannan

Naziru Sarkin Waka ya tubewa 'Yan wasan fim zani a kasuwa yayin da ya kare Almajirai

Mawakin ya kara da cewar wasu daga cikin masu martanin ma ko cikakkiyar Fatiha ba za su iya kawowa ba amma suke zagin almajirai wanda a cikinsu harda wanda ya rubuta Al-Kur’ani.

Asali: Legit.ng

Online view pixel