Mai neman suna: Idan ka isa ka bugi kirji ka kira suna, Nafisa ga Sarkin Waka

Mai neman suna: Idan ka isa ka bugi kirji ka kira suna, Nafisa ga Sarkin Waka

  • Jaruma Nafisa Abdullahi ta yi martani mai zafi ga Sarkin Waka kan wallafar da yayi na kare iyayen da ke haihuwar yara su barsu suna almajiranci
  • Jarumar ta kira Naziru Sarkin Waka da mai neman suna, ta kara da cewa ta san matsalarsa kuma idan ya isa, ya bugi kirji ya kira suna ne
  • A cikin makon nan ne Nafisa ta caccaki iyaye da ke haihuwar yara babu kulawa suna sakinsu a titi inda suke zama almajirai

Jaruma Nafisa Abdullahi ta yi martani ga fitaccen mawaki, Naziru Ahmad wanda aka fi sani da Sarkin Wakar San Kano.

A jiya ne mawakin yayi wata wallafa wacce kai tsaye wadanda ke bibiyar shafin jaruma Nafisa Abdullahi za su gane cewa martani ne yayi ga wata wallafar da tayi.

Kara karanta wannan

Naziru Sarkin Waka ya tubewa 'Yan wasan fim zani a kasuwa yayin da ya kare Almajirai

Jarumar ta caccaki iyayen da ke haihuwa tare da kin daukar dawainiyar 'ya'yan kuma su sake su a kan titi suna almajiranci babu tarbiya.

Babu shakka wannan wallafa ta tada kura inda 'yan Najeriya ballantana arewaci aka yi caa a kanta.

Mai neman suna: Idan ka isa ka bugi kirji ka kira suna, Nafisa ga Sarkin Waka
Mai neman suna: Idan ka isa ka bugi kirji ka kira suna, Nafisa ga Sarkin Waka. Hotuna daga @nafeesat_official/@sarkin_wakar_san_kano
Asali: Instagram

Kwatsam sai ga wallafar Sarkin Waka inda yake bayyana cewa ba almajirai bane yaran da iyayensu suka haifa suka kasa kula da su ba, idan kana son ganin 'ya'yan da iyayensu suka haifa kuma suka kasa kula dasu, toh ka taho masana'antar fim.

Jaruma Nafisa Abdullahi bata yi kasa a guiwa ba taje shafinta na Twitter inda ta yi wa mawakin martani inda ta kira shi da mai neman suna. Idan kuma ya isa, ya bugi kirji ya kira suna.

Ga martanin nata:

Kara karanta wannan

Kin jinin Musulmi: China ta yi Allah wadai da wadanda suka kona al-Qur'ani a Sweden

"Mai neman suna!!! Ka bugi kirji ka kira suna mana. Duk da dai na san matsalarka. Ramadan Kareem."

Naziru Sarkin Waka ya tubewa 'Yan wasan fim zani a kasuwa yayin da ya kare Almajirai

A wani labari na daban, shahararren mawakin nan, Naziru M. Ahmed ya yi rubutu, yana cewa almajiranci da iyaye suke aika yara ya na da amfani, kuma sun ci moriyar hakan. Sarkin Waka ya ce tura yara karatu da iyaye suke yi, ya fi a kan a kyale su da makamai a cikin jeji.

"Wannan shine gaskiya malamai. Ko tayi dadi, ko kar tayi dadi. Kowa ya dauko sharrinsa sai kan almajirai da iyayensu??
To mu munsan abin da kuke kira da almajirci duk da ba sunansa kenan ba, mun san niyyar da ke sa iyaye su kai ‘ya ‘yansu, mun kuma ga amfaninsa.
Watau kun fi so a bar yara a daji babu manufa ayi ta ba su bindigu suna kashe mu? Wannan shine burinku??"

Kara karanta wannan

Daga Landan zuwa Lagas: 'Yan Najeriya 3 da suka yi tafiyar ban mamaki a kafa da babur

Asali: Legit.ng

Online view pixel