Babu wacce iyayenta basu san yadda za su yi da ita ba sama da macen da za ta kama otel tana iskanci - Naziru

Babu wacce iyayenta basu san yadda za su yi da ita ba sama da macen da za ta kama otel tana iskanci - Naziru

  • Mawaki Naziru sarkin waka ya yi hannunka mai sanda ga abokiyar sana’arsa Nafisa Abdullahi bayan ta kalubalanci Almajiranci
  • Sarkin Waka ya ce babu wanda iyayensa suka haife sa suka rasa yadda za su yi da shi sama da macen da za ta dunga kama otel tana iskanci tana turawa duniya
  • Ya ce abun da ya fi bashi haushi shine ace mutumin da ba zai iya karanta Fatiha yadda take ba amma yana zagin almajirai da wasun su sun rubuta Al-Qur’ani

Shahararren mawaki, Naziru Sarkin waka ya sake yin zazzafan martani a kan furucin da jaruma Nafisa Abdullahi ta yi kan Almajirai da iyayensu.

Sarkin waka ya nuna bacin ransa, inda ya bayyana cewa babu wanda iyayensa suka yi asarar haihuwarsa sama da mutumin da zai sunga iskanci yana sakin hotuna duniya na zaginsa amma shi ko a jikinsa.

Kara karanta wannan

Kullun burinka ka zagi yan fim: Maryam Booth ta yi martani ga Naziru sarkin waka

Mawakin ya kara da cewar wasu daga cikin masu martanin ma ko cikakkiyar Fatiha ba za su iya kawowa ba amma suke zagin almajirai wanda a cikinsu harda wanda ya rubuta Al-Kur’ani.

Babu wacce iyayenta basu san yadda za su yi da ita ba sama da macen da za ta kama otel tana iskanci - Naziru
Babu wacce iyayenta basu san yadda za su yi da ita ba sama da macen da za ta kama otel tana iskanci - Naziru Hoto: sarkin_wakar_san_kano
Asali: Instagram

A cikin wani bidiyo da ya wallafa a a shafinsa na Instagram, Naziru ya kuma ce wadanda iyayensa suka yi asarar haihuwarsa it ace wacce za ta tafi uwa duniya ta kama otel tana abubuwan da ta ga dama.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce:

"Tsari da jama’a idan zan yi magana ko idan na yi magana sai a ce bana son zaman lafiya, ba haka bane ba. Idan dai z aka fadi gaskiya ne ake fadar haka amma idan z aka fadi wani abu makamancin haka bah aka bane, kuma bana fada don wani ya ji haushi, ban taba fada domin in ta da hazo ba, ban kuma fada don wani ya dubi shafina ba babu abun da ya shafe ni da wannan ni koda yasushe fejina a cikin godiyar Allah take.

Kara karanta wannan

Mai neman suna: Idan ka isa ka bugi kirji ka kira suna, Nafisa ga Sarkin Waka

“Abun da ya bani haushi shine wai yau ace mutum da ba zai iya karanta Fatiha ba cikakkiya yadda take wai shine za a dunga amfani da shi wai ana cewa wai akwai wasu wanda iyayensu sun haife su basu san yadda za su yi da su ba.
“Wadannan kuma da ake gayawa iyayensu sun haife su basu san yadda za su yi da su ba wani ma ya rubuta Kur’ani, wani yana kan rubutawa, wani ya haddace izuzuka, sune Almajiran da ake magana.
“Jama’a dan Allah wanda iyayensa suka haife shi basu san yadda za su yi da shi ba ya wuce wanda haka kawai zai yi iskanci ya turowa duniya tana gani ai ta tsine masa ko a jikinsa yana dariya, yana ganin shi yayi daidai.
“Akwai wanda iyayensa suka haife shi basu san yadda za su yi da shi ba ya wuce mutumin da haka kawai zai tashi ya tafi chan, in mace ce ta je ta kame gida ko otel kullun tana otel.

Kara karanta wannan

Naziru Sarkin Waka ya tubewa 'Yan wasan fim zani a kasuwa yayin da ya kare Almajirai

“Duk iyeyen duniya karya ne ba a san ransu bane idan ba karatu ba, ko karatu da kaga ana kai yara Turai rashin makarantun ne a nan. Idan ba karatu ba babu uwar ko uban da za ta so ace tana kwana gida yarta na chan wani waje tana abu da bata ma san menene ba, wai sana’a ta rufe ta. Ko kuma wani yana nan ya zama kartagi na yan iska shine ke tara su kuma shina hakan yake, kuma bashi ma da niyan rabuwa da su ko shi ya bar abun da yake yi toh duk wannan ba ace iyayen su sun yi asarar haihuwarsu ba sai mutanen da ake kira almajirai."

Jama'a sun yi martani:

iamumaryaro ya ce:

"Kai dai kana da Personal matsala da wanda tayi wannan magana ne kawai. Amma zancen gaskiya maganar ta yana kan hanya."

mcubed4real ya yi martani:

"A ina aka ce ka kai yaron ka karatu inda kana da yakinin cewa bazai sami tarbiyya da kulawa ba? Ai ita gaskiya daya ce ko a bakin waye tafito kawai ka dauketa. Tsarin karatu tsangaya ya lalace, daban take da na da Dole a gyarata ko kuma ko wani yaro yayi karatu a gaban mahaifansa."

Kara karanta wannan

Da Farko Kallon Mahaukaci Ake Min: Mutumin Da Ya Zama Miloniya Da Sana'ar Sayar Da Ƙarafuna Masu Tsatsa Legas

fulanyboy ya ce:

"Gaskia kuma Daman Daya ce Daga kinta sai Bata Kuma duk wanda yasanta ya kuma taketa,Toh Tabbas Ya Bata "

sutura_empire ya ce:

"Da kyau mutumina ka cigaba da kula da wannan barin..❤️, ita nafisa da hannu kamar wada almajirai sunfi ta daraja, sai shegen girman kai kamar wata sarauniyar ingila"

Naziru Sarkin Waka ya tubewa 'Yan wasan fim zani a kasuwa yayin da ya kare Almajirai

A baya mun ji cewa Naziru M. Ahmed ya yi rubutu, yana cewa almajiranci da iyaye suke aika yara ya na da amfani, kuma sun ci moriyar hakan.

Sarkin Waka ya ce tura yara karatu da iyaye suke yi, ya fi a kan a kyale su da makamai a cikin jeji.

Asali: Legit.ng

Online view pixel