YBN da 13X13: Sabuwar baraka ta kunno kai a masana'antar Kannywood gabannin zaben 2023

YBN da 13X13: Sabuwar baraka ta kunno kai a masana'antar Kannywood gabannin zaben 2023

  • Gabannin 2023, sabuwar baraka ta kunno kai tsakanin masu ruwa da tsaki a masana’antar Kannywood ta fuskar siyasa
  • Barakar dai ya samo asali ne daga kungiyoyin YBN da 13X13 wadanda aka kirkira a cikin masana'antar fim din
  • Sai dai babban darakta Falalu Dorayi ya shawarci shugabannin kungiyoyin a kan kada su ba shaidan damar da zai shiga tsakaninsu ko ya haddasa gaba a cikinsu

Kamar yadda aka saba, a duk lokacin da siyasa ta kawo jiki, manyan jaruman masana’antar shirya fina finan Hausa ta Kannywood maza da mata kan tsunduma a harkar siyasa tare da tallata yan takara daban-daban.

Gabannin babban zaben 2023, akwai alamu da ke nuna akwai barakar da ta kunno kai a masana'antar ta Kannywood.

Kara karanta wannan

Hadimin Buhari: Zaben 2023 zai fi kowane zabe zama sahihi saboda kokarin Buhari

YBN da 13X13: Sabuwar baraka ta kunno kai a masana'antar Kannywood
YBN da 13X13: Sabuwar baraka ta kunno kai a masana'antar Kannywood Hoto: saratudaso/generalbmb4pmb
Asali: Instagram

A wannan karon, lamarin ya fito ne daga wasu kungiyoyi biyu da aka kafa a cikin masana'antar.

Kungiyoyin YBN da 13X13

Kungiyar YBN wato 'Yahaya Bello Network' an kafa ta ne saboda aniyar takarar shugabancin gwamnan jihar Kogi. Kuma jaruman Kannywood sune kan gaba a wannan kungiya wacce Abdul Amart ke jagoranta.

Hakazalika akwai kungiyar mawaka da Dauda Kahutu Rarara ya kafa mai suna 13X13, wacce suka ce an kirkireta ne domin taimakon talakawa ba wai don siyasa ba.

Alamu sun nuna akwai baraka a tsakanin wadannan kungiyoyi biyu duba ga irin habaice-habaice da ke tashi a shafukan soshiyal midiya.

BMB ya yi martani

Bello BMB wanda jarumi ne a masana'antar kuma dan gaba a kungiyar YBN ya yi wata wallafa a shafinsa inda ya ce ba gasa suke yi da kowa ba.

Kara karanta wannan

Mun yi ittifaki, Wajibi ne wanda zai gaji Buhari ya kasance Kirista daga kudancin Najeriya: CAN

Ya rubuta:

“Ba gasa muke yi da kowa ba, bama sha’awar shan kashi domin muna son kayar da ku ne, kada ku yi kokarin kayar da mu domin mu ba za a iya kayar da mu ba.
Idan ba za ku iya doke mu ba, ku hada hannu tare da mu, har yanzu akwai sauran guraren da ba kowa saboda ku."

Falalu Dorayi ya ja hankalin shugabannin kungiyoyin biyu

A nashi bangaren babban darakta kuma Jarumi, Falau A. Dorayi ya je shafinsa na Instagram don jan hankalin shugabannin kungiyoyin a kan kada su bata rawarsu da tsalle.

A wallafar tasa, Falalu ya ce shi a ganinsa aikin kungiyoyin daya ne wato taimakon al’umman ciki da wajen masana’antar, sannan ya ce kada wani daga cikinsu ya bari shaidan ya ci galaba a kansu ta hanyar jefa su cikin gaba.

Falalu ya rubuta a shafin nasa:

“A mahanga ta, Duk kungiyoyin suna aiki ne kusan iri daya, Taimakon mutanen Masana’antar da Mutanen wajanta. Wannan Abu ne da idanu suka gani suka tabbatar.

Kara karanta wannan

2023: Dattawan Arewa Sunyi Taro, Sun Yanke Shawarar Goyon Bayan Igbo Ya Maye Gurbin Buhari

“Shawara ce domin masalaha. Karku bawa shaidan dama wajan shiga tsakaninku, kuma Kar ku bawa zuciya dama ta jefa muku gaba ko kiyayya.
“Kuyi komai domin Allah. Kar ku bada gurbin haibaici tsakaninku. Ku nuna dattaku ku cigaba da samar da alkairi da yadashi a tsakanin mabukata. WANNAN DABI’ACE TAGARI.
“Abin alfahari Kannywood ta hada ku cikin Sana’a da neman. Kafin zuwan kungiyoyin. Abokan juna ne ku, Sana’arku daya, Wajan zamanku daya, Kuna kwana guri daya tare, Kuci abinci tare a kwano daya. Hakan ya nuni da kauna, zumunci da abokantaka.
“Duk wata alfarma da arziki da yake tare damu Mun same shi sanadin Kannywood. Me zai hana ku maida hankali wajan godiya ga Allah da cigaba da taimakon da kuka saba, maimakon kokarin bawa Shaidan dama ya haifar da gaba.
“Da kaunar Juna muka zo duk inda muke, Da kaunar juna ne zamu wuce inda muke a Yanzu.
“Ina rokon Jagororin kungiyoyin, Ina gama ku da Allah da Annabi. Kuyi duba da Alkairin da kuke rabawa da farin ciki da suke sakawa a zukata masu yawa, kuyi aiki da hankali kar ku bari Shaidan yai haifar da gaba da habaici tsakaninsu.

Kara karanta wannan

Rikicin Masarautar Kano da Kamfanin jirgi: Ya kamata manya su saka baki, inji wata kungiya

“Abu Hurairah yace: RASULULILAH (S.A.W) yace:
"Ba zaku shiga Aljanna ba har sai kun yi imani, Ba zaku yi Imani ba har sai kuna son junan ku, Shin kuna son in yi muku nuni da abun da idan kuka aikata shi zaku so junan ku? Ku yada sallama tsakanin ku" Muslim:54
“Nazo da Aminci. Amincin Allah ya tabbata a gareku.”

Hotunan manyan yan Kannywood yayin da suka gana da mataimakin shugaban kasa a Villa

A gefe guda, mun kawo a baya cewa manyan jaruman masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood sun ziyarci fadar shugaban kasa da ke babbar birnin tarayya Abuja.

A yayin ziyarar da suka kai a ranar Alhamis, 17 ga watan Fabrairu, sun saka labule tare da mataimakin Shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo.

Sun yi tafiyar ne karkashin kungiyarsu mai suna 13X13, wacce suka ce an kafa ta ne domin taimakon al’umma.

Kara karanta wannan

Shugaban kasa a 2023: Wata kungiyar arewa ta goyi bayan Jonathan ya tsaya takara

Asali: Legit.ng

Online view pixel