Hotunan manyan yan Kannywood yayin da suka gana da mataimakin shugaban kasa a Villa

Hotunan manyan yan Kannywood yayin da suka gana da mataimakin shugaban kasa a Villa

  • Wasu jaruman Kannywood sun ziyarci mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo a fadar shugaban kasa da ke Abuja
  • A yayin ziyarar tasu karkashin inuwar kungiyarsu mai suna 13X13 sun sanya labule da mataimakin shugaban kasar
  • Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da lamuran siyasa suka fara kankama a kasar gabannin babban zaben 2023

Manyan jaruman masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood sun ziyarci fadar shugaban kasa da ke babbar birnin tarayya Abuja.

A yayin ziyarar da suka kai a ranar Alhamis, 17 ga watan Fabrairu, sun saka labule tare da mataimakin Shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo.

Hotunan manyan yan Kannywood yayin da suka gana da mataimakin shugaban kasa a Villa
Hotunan manyan yan Kannywood yayin da suka gana da mataimakin shugaban kasa a Villa Hoto: saratudaso
Asali: Instagram

Sun yi tafiyar ne karkashin kungiyarsu mai suna 13X13, wacce suka ce an kafa ta ne domin taimakon al’umma.

Daga cikin jaruman da suka yi wannan tafiya akwai Saratu Gidado wacce aka fi sani da Daso, Maryam Booth, Yakubu Muhammad, Mustapha Naburaska, Baban Chinedu.

Kara karanta wannan

Direbobin Keke-Napep sun yi wa Osinbajo mubaya’a ya dare kujerar Shugaban kasa

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sauran sun hada Teemah Makamashi, Aisha Humaira, babban furodusa, Bashir Mai Shadda, mawaki Daudu Kahuta Rarara, Aminu Ahlan waka, Rabiu Rikadawa, Salisu Fulani da dai sauransu.

Daso ta wallafa hotunan ganawar tasu a shafinta na Instagram inda aka gano mataimakin Shugaban kasar a tsakaninsu.

Kalli hotunan ganawar tasu a kasa:

Kungiyar MOPPAN ta gargadi yan Kannywood da su daina kwancewa juna zani a kasuwa

A wani labarin, kungiyar masu shirya fina-finan Hausa ta Najeriya (MOPPAN), ta gargadi yan wasan Kannywood da su daina kwancewa junansu zani a kasuwa musamman a shafukan soshiyal midiya.

Wannan jan kunnen ya biyo bayan rikicin da ya kunno kai a masana’antar cikin yan kwanakin da suka gabata.

A wata sanarwa dauke da sa hannun kakakinta, Al-Amin Ciroma, kungiyar ta ce ta ga akwai bukatar takawa yan wasan birki ne a yayin da ake ci gaba da kace-nace dangane da rigingimun da suka biyo bayan tattaunawar da BBC Hausa ta yi da Hajiya Ladin Cima.

Kara karanta wannan

Mun fi karfin mataimakin shugaban kasa, dole a ba mu kujerar shugaban kasa - Kungiyar Ibo

Asali: Legit.ng

Online view pixel