Mun fi karfin mataimakin shugaban kasa, dole a ba mu kujerar shugaban kasa inji Kungiyar Ibo

Mun fi karfin mataimakin shugaban kasa, dole a ba mu kujerar shugaban kasa inji Kungiyar Ibo

  • Fitattun mutane daga kasar Ibo karkashin inuwar Igbo Elders Consultative Forum sun yi wani taro
  • Kungiyar IECF ta bayyana muradin da ta ke da shi a zaben shugaban kasa mai zuwa da za ayi a 2023
  • Chukwuemeka Ezeife ya yi jawabi, ya gargadi Ibo a kan neman kujerar mataimakin shugaban kasa

Jaridar Vanguard ta ce kungiyar Igbo Elders Consultative Forum ta yi zama a ranar Laraba, 16 ga watan Fubrairu 2022, inda suka yanke shawara a kan takarar 2023.

Kungiyar ta ce dole ne shugaban kasa na gaba da za ayi, ya fito daga yankinsu na kudu maso gabas.

Abin bai tsaya nan ba, kungiyar Ibon ta ce za ta dauki hukunci mai tsanani kan duk wani ‘dan siyasar Ibo da ya yarda da tayin takarar mataimakin shugaban kasa.

Kara karanta wannan

IBB ga 'yan siyasa: Kar ku yi wasa da hadin kan 'yan Najeriya

A cewar manyan na kasar Ibo, ya zama dole shugaban kasa ya fito daga shiyyar Kudu maso gabashin kasar nan ko kuma duk su hakura, su fice daga Najeriya.

Shugaban IECF, Dr. Chukwuemeka Ezeife ya bayyana wannan da ya zanta da ‘yan jarida a Abuja.

Sun ta ce sauran wadanda aka yi wannan zama da su sun hada da Farfesa Ihechukwu Madubuike; Dr. Kingsley Nkonye; Igwe Ibe Nwosu da wasu manyan.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Zaben shugaban kasa
Peter Obi ya na kamfe a 2019 Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

“Mu na jiransu (jam’iyyun siyasa), za su gamu da matsala idan wannan karo suka ajiye mutanen kudu maso gabas a gefe, suka hana mu fito da shugaban Najeriya a 2023.”

- Chukwuemeka Ezeife

Ku fito takara - Chukwuemeka Ezeife

Chukwuemeka Ezeife ya yi kira ga ‘yan siyasarsu masu hangen nesa da basira su tsaya takara, la'akari da yadda kiraye-kiraye suka yi yawa na ganin sun karbi mulki.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: Jonathan Ya Goyi Bayan Gwamnan PDP Ya Zama Shugaban Ƙasa a 2023

Ezeife ya ce ba za su yi sauki ga ‘dansu da ya bari ya zama abokin takarar wani daga wajen yankin Kudu maso gabas a 2023 ba, ko a ba su mulki, ko su fice daga kasar.

A ba mu a huta - Charles Nwekeaku

Bayan jawabin tsohon gwamnan na jihar Anambra, Chukwuemeka Ezeife, sakataren kungiyar, Charles Nwekeaku ya yi magana ya na mai jan-kunnen jam’iyyun siyasa.

Farfesa Charles Nwekeaku ya ce duk jam’iyyar da ba ta ba mutumin kudu maso gabas tutar takarar shugaban kasa a zaben na 2023, to ta hakura da kuri’un ‘Yan Ibo.

Siyasar APC

Kwanan nan ne aka ji cewa Rauf Aregbesola wanda tun a 1999 yake tare da Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya fito gaban Duniya ya nuna zai yake shi a zaben Gwamnan Osun.

Tsohon Gwamnan Osun Rauf Aregbesola da mutanensa sun ja layi, za su gwabza da Bola Tinubu, su hana Gwamna mai-ci, Gboyega Oyetola samun tazarce a zaben 2022.

Kara karanta wannan

Shugaban kasa a 2023: Atiku ya samu gagarumin goyon baya daga wata kungiyar Inyamurai

Asali: Legit.ng

Online view pixel