Direbobin Keke-Napep sun yi wa Osinbajo mubaya’a ya dare kujerar Shugaban kasa

Direbobin Keke-Napep sun yi wa Osinbajo mubaya’a ya dare kujerar Shugaban kasa

  • Wata kungiya ta direbobin Keke Napep ta karfafawa takarar Farfesa Yemi Osinbajo a zaben 2023
  • Kungiyar magoya baya ta Osinbajo Support Movement ta ziyarci jagororin TOAN a hedikwatarta
  • Shugaban TOAN na kasa ya bayyana cewa za su marawa mataimakin shugaban Najeriya baya a zabe

Abuja - Kungiyar direbobin Keke Napep a Najeriya watau TOAN ta yi wani zama na musamman a ranar Talata, 15 ga watan Fubrairu 2022 a kan siyasa.

Jaridar PM News ta ce kungiyar TOAN ta bayyana cewa ta na tare da mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo a takarar shugaban kasar da za ayi.

Kungiyar ta bayyana goyon-bayanta ga Yemi Osinbajo ne a lokacin da shugabannin tafiyar Osinbajo Support Movement (OSM) suka kawo mata ziyara.

A makon nan jagororin Osinbajo Support Movement su ka gana da shugabannin kungiyar TOAN a hedikwatarsu da ke unguwar Gwarinpa a babban birnin Abuja.

Kara karanta wannan

Mun fi karfin mataimakin shugaban kasa, dole a ba mu kujerar shugaban kasa - Kungiyar Ibo

Shugaban tafiyar OSM da ke goyon bayan takarar Osinbajo watau Liberty Badmus da shugaban mata na kungiya, Aisha Muazu suka yi zama da direbobin.

Shugaban kasa
Shugaba Buhari da Farfesa Yemi Osinbajo Hoto: www.vanguardngr.com
Asali: UGC

Mu na tare da ku - Tata Sule

Alhaji Shehu-Tata Sule wanda shi ne shugaban direbobin Keke Napep na kasa da wasu ‘yan kungiyarsa duk sun nuna suna tare da kungiyar OSM a zaben 2023.

Shehu-Tata Sule ya bayyana cewa akwai bukatar kungiyoyin biyu su samu alaka mai karfi domin ganin yadda za su cinma burinsu na tallata Osinbajo a Najeriya.

Pulse ta ce Sule ya yi wa masoya mataimakin shugaban alkawari za su yi kokari wajen bada gudumuwa da karfinsu da kayan aiki don hakarsu ta cin ma ruwa.

“Mun samu kwarin-gwiwa, kuma mun gamsu mu mara baya ga Farfesa Osinbajo saboda kishin kasar da yake nunawa a lamura, game da sanin aikin da ya yi.”

Kara karanta wannan

Rikicin APC a Kano: Dattawan jihar sun shiga tsakanin tsagin Ganduje da Shekarau

“Har da kuma la’akari da halayya, kwarjini, tsayin-daka, adalci da kokarinsa na daukar matakin da ya kamata domin cigaban al’umma.” - Shehu-Tata Sule.

Liberty Badmus ya yi jawabi ya na mai farin cikin wannan goyon baya da suka samu a tafiyarsu.

Lokacin Ibo ya yi

Dazu nan aka ji labari shugaban Igbo Elders Consultative Forum yana barazanar cewa idan har mutumin Ibo bai zama Shugaban kasa ba, za su fice daga kasar nan.

Manyan na kasar Ibo sun ce babu abin da za su yi da takarar mataimakin shugaban kasa a zaben 2023, sai dai a damka masu mulkin Najeriya ko su ki zaben jam'iyya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel