Kano: Sadiya Haruna ta sha da kyar hannun Ƴan daba, sun yi yunƙurin watsa mata acid

Kano: Sadiya Haruna ta sha da kyar hannun Ƴan daba, sun yi yunƙurin watsa mata acid

  • Jarumar Kannywood mai siyar da kayan mata, Sayyada Sadiya Haruna, ta koka kan yadda wasu matasa 2 suka kusan watsa mata acid a daren Juma'a
  • A bidiyon da ta saki a shafin ta na Instagram, Sadiya Haruna ta bayyana yadda matasan suka biyo ta bayan ta tashi daga shago amma ta sha kyar
  • A cikin bidiyon, jarumar ta kira sunan wasu mutum biyu "Anty mai tusar jaki" da "wannan azzalumin" a matsayin wadanda ta ke zargi da farautar ta

Kano - Fitacciyar jaruma, Sayyada Sadiya Haruna, ta saki wani bidiyo inda ta koka kan wasu 'yan daba a birnin Kano sun yi yunkurin watsa mata acid a fuska a ranar Juma'a, 28 ga watan Janairu.

Cike da tashin hankali yayin da ta ke kuka tare da ihu ta yi bidiyon a cikin mota, inda wani matashi wanda ta kira da Besty ya ke jan ta.

Kara karanta wannan

Na kasa daina sata: Matar da ta fara sata tun tana shekaru 7 ta ba da tarihin rayuwarta

Kano: Ƴan daba sun yi yunƙurin watsa wa Jaruma Sadiya Haruna acid
Kano: Ƴan daba sun yi yunƙurin watsa wa Jaruma Sadiya Haruna acid. Hoto daga @sayyada_sadiya_haruna
Asali: Instagram

A cewar Sadiya Haruna kamar yadda ta wallafa a shafin ta na Instagram, ta taso daga shagon ta inda ta ce wa kanin ta za ta biya kanti domin siyayya, shi ya karasa gida kafin ta iso.

Kwatsam sai ta ji wasu matasa da ke biye da ita suna cewa, "ka watsa mata mu gudu" lamarin da ta ce ya firgita ta kuma ta hanzarta kaiwa motar ta tare da rufe kanta.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kamar yadda tace:

"Na tashi daga shago na da karfe 7:47 na yamma, zan bi ta Hama store in siya abu kafin in wuce gida, sai na cewa kani na ya hau Keke a wuce da shi gida. Ina fitowa daga shago na sai na ga wasu maza guda biyu, sai daya yake cewa ka watsa mata mu gudu.

Kara karanta wannan

Tattaki: Yadda bature ya taso daga Landan zuwa Makka da kafa, ya fadi manufarsa

"Ina jin haka na shiga mota ta na saka central lock, ban san ko ina a garin Kano ba, banda gida na da ofis babu inda na ke zuwa. Ko wani wuri na ke son zuwa sai Besty ne ya ke kai ni. Nan na kubucewa bayin Allah da ke son watsa min acid.
"Wuraren karfe takwas na fara kiran kani na bayan mun gama zagaye da su. Umar ba ya daukan kiran shi. Daukan kiran shi da zai yi yace Anty ki gudu akwai matsala."

Sai dai a cikin bidiyon, Sadiya Haruna ta dinga kiran wasu abokan sana'ar ta wadanda a kwanakin baya suka samu matsala da su.

Ta kira "Anty mai tusar jaki" da kuma "wannan azzalumin" inda tace ta ga motar su a kofar gidan ta.

Kotun Musulunci a Kano ta yanke wa jaruma Sadiya Haruna hukunci

Kara karanta wannan

Yadda wani ya sa aka yi garkuwa da ‘yaruwarsa ta jini wajen neman abin Duniya a Kaduna

A wani labari na daban, hukumar Hisbah ta jihar Kano ta damki jarumar Kannywood, kuma sun garkame ta sakamakon yada hotunan batsa da take yi a shafukanta na kafafen sada zumunta.

Kamar yadda BBC Hausa ta ruwaito, tun ranar Juma’a jami’an hukumar suka kama ta tunda dama ita mazauniyar Kabuga ce dake jihar Kano.

Shafin Linda Ikeji ya ruwaito cewa, sun cigaba da rike ta har ranar Litinin kafin suka mika ta zuwa kotun musulunci don a yanke mata hukunci a Sharada.

Asali: Legit.ng

Online view pixel