Yadda wani ya sa aka yi garkuwa da ‘yar uwarsa ta jini wajen neman abin Duniya a Kaduna

Yadda wani ya sa aka yi garkuwa da ‘yar uwarsa ta jini wajen neman abin Duniya a Kaduna

  • Wata ‘yar kasuwa da ke zaune a garin Zaria, jihar Kaduna ta na shari’a da ‘danuwanta a gaban Alkali
  • Binta Mohammed ta bada labarin yadda wannan ‘danuwan nata ya sa aka yi garkuwa da ita a Zaria
  • Wannan matar ta na zargin Abubakar Haliru da damka ta hannun wadanda suka yi garkuwa da ita

PM News ta rahoto Hajiya Binta Mohammed ta na shaidawa babban kotun jihar Kaduna da ke Dogarawa cewa Abubakar Haliru ya kitsa dauke ta da aka yi.

Ana zargin Abubakar Haliru wanda kakansu daya da wannan ‘yar kasuwa da shirya yadda za a sace ta. Wannan laifi ya saba sashe na 246 na dokar final kwad.

Lauyar da ta shigar da kara a kotun na Dogarawa da ke Zaria, Jummai Dan-Azumi ta ce ta na da shaidu hudu da za su bada shaida, ta fara da Binta Mohammed.

Kara karanta wannan

Yadda yunkurin zawarcin Jonathan, a ba shi takara a APC ya sha ruwa tun kafin a kai 2023

Kamar yadda Today.ng ta kawo rahoto, Mohammed ta fadawa Alkali cewa ta na zama ne a unguwar GRA Zaria, kuma Abubakar Haliru ‘danuwanta ne.

Mohammed ta nemi Haliru ya biya ta kudinta na tukin Keke Napep. Daga karshe ya nemi su je wajen wani mutumi a unguwar Danmagji domin a karbi kudin.

'Yan sanda
Jami'an 'Yan sanda Hoto: freedomradionig.com
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Na bi shi Danmagaji a mota

Wannan Baiwar Allah ta ce da farko ba tayi niyyar zuwa wajen kowa ba, amma daga baya ta yarda ta bar shagonta, ta bi shi a cikin mota domin ta yarda da shi.

Yayin da ta ke tsammanin za a tsaya a Danmagaji, sai Binta Mohammed ta ga Haliru ya cigaba da tafiya, ya yi waya da wasu, ya ce za su karaso nan da 'yan mintuna.

Su na cikin tafiya sai ga wasu a gefen titi dauke da bindigogi, daga nesa ta hango wasu da makamai.

Kara karanta wannan

Baturiya mai auren ‘Dan Najeriya ta rangada ado, ta ci ankon atamfa da yara da mai gidanta

Ya kai ni wajen miyagu

“Sai na fada masa ya juya domin mu gujewa wadannan miyagun mutane, amma ya dage sai ya tsaya da mota kusa da wadannan mutane biyu masu bindiga."

- Hajiya Mohammed

A nan take masu garkuwa da mutane suka yi ram da ita, aka karbe mata jaka, waya, katin ATM, katin zabe, mubudi, da kudi, amma ba a taba ‘dan uwan na ta ba.

Daga nan aka wuce da ita zuwa wani tsauni, da ta nemi a kyale ‘danuwanta, ta ce sai aka doke ta.

Daga N100m, an koma neman N300m

‘Yan bindiga sun nemi a biya N100m kafin ta fito, amma a karshe ta tsere, kuma ta fada hannun wasu da suka nemi a biya N300m kafin a sake ganinta a Duniya.

Mohammed ta fadawa mai shari’a Kabir Dabo, sai da tayi makonni takwas a tsare, aka biya fansar N5.5m baya ga katin waya na N700, 000 da wayoyin salula biyu.

Kara karanta wannan

Labari ne mai ban tsoro - Dattawan arewa sun yi Allah wadai da kisan Hanifa

Wanene ya kashe Abiola?

Bayan shekara da shekaru ana zargin guba aka ba Cif MKO Abiola ya ci, ya mutu a shekarar 1997, Janar Abussalami Abubakar ya bada cikakken labarin abin da ya faru.

Da aka zanta da shi, Abdussalami yace Abiola ya fara rashin lafiye ne yayin da yake ganawa da wasu Amurkawa, daga nan aka kai shi asibiti, a haka ya cika inji

Asali: Legit.ng

Online view pixel