Kotun Musulunci a Kano ta yanke wa jaruma Sadiya Haruna hukunci

Kotun Musulunci a Kano ta yanke wa jaruma Sadiya Haruna hukunci

  • Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta damki wata ‘yar wasan kwaikwayo na Kannywood, Sadiya Haruna wacce ta shahara a kafafen sada zumunta
  • Hukumar ta kama ta ne bisa laifin yada hotuna da kalaman batsa a shafukanta na sada zumuntar zamani tun ranar Juma’a har ranar Litinin
  • Bayan ta amsa laifinta ne aka yanke mata hukumcin komawa Islamiyya ta yi karatun addini har na tsawon watanni shida

Kano - Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta damki jarumar Kannywood, kuma sun garkame ta sakamakon yada hotunan batsa da take yi a shafukanta na kafafen sada zumunta.

Kamar yadda BBC Hausa ta ruwaito, tun ranar Juma’a jami’an hukumar suka kama ta tunda dama ita mazauniyar Kabuga ce dake jihar Kano.

Kotun Musulunci a Kano ta yanke wa jaruma Sadiya Haruna hukunci
Kotun Musulunci a Kano ta yanke wa jaruma Sadiya Haruna hukunci. Hoto daga @sayyada_sadiya_haruna
Asali: Instagram

Shafin Linda Ikeji ya ruwaito cewa, sun cigaba da rike ta har ranar Litinin kafin suka mika ta zuwa kotun musulunci don a yanke mata hukunci a Sharada.

Kara karanta wannan

Hisbah ta garkame Jarumar Kannywood kan saka al'amuran baɗala a kafar sada zumunta

Sadiya ta amsa laifi daya ciki tarin laifukan da ake zarginta da aikata wa wanda hakan ya ci karo da sashi na 355 na kundin Penal code na 2000.

Alkali Ali Jibril Danzaki ya yanke mata hukunci tare da umartar ta da komawa Islamiyya don ta yi karatu na tsawon watanni shida.

Sannan dole ne kullum jami’an Hisbah za su dinga rakata zuwa Islamiyyar domin tabbatar da ta je Islamiyyar sannan shugaban makarantar zai kiyaye da zuwanta.

Obasanjo ya yi addu'ar Allah ya ɗauki ransa: Na ga uku, bana addu'ar ganin Olu na Warri na huɗu

A wani labari na daban, tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo da Gwamna Ifeanyi Okowa na Jihar Delta, a ranar Lahadi sun jagoranci manyan mutane da dama zuwa hallartar addu'ar ban godiya na nadin sarautar Mai Martaba Ogiame Atuwatse III, rahoton Arise News.

Kara karanta wannan

Jaruma Ummi Rahab ta gargadi Adam Zango, ta yi barazanar tona masa 'asiri'

Da ya ke magana wurin taron, Obasanjo ya bukaci sabon sarkin na Itsekiri ya yi aiki domin hada kan masarautarsa da ma Nigeria baki daya.

Tsohon shugaban kasar ya ce ya yi matukar sa'an ganin nadin sarautan Olu guda uku, yana mai cewa baya fata ko addu'ar ganin nadin wani Olun na Warri, Arise News ta ruwaito.

Ya yi wa sabon sarkin addu'a, yana mai cewa Allah ya ja zamaninsa cikin zaman lafiya, ya kuma bashi ikon hada kan al'umma da kawo cigaba a kasar Itsekiri.

Asali: Legit.ng

Online view pixel