Masana’antar shirya fina-finai: Jerin jaruman Kannywood 10 da asalinsu ba Hausawa bane

Masana’antar shirya fina-finai: Jerin jaruman Kannywood 10 da asalinsu ba Hausawa bane

  • Masana'antar shirya fina-finai ta Kannywood na daya daga cikin manyan masana'antu masu muhimmanci a yankin arewacin kasar
  • Kannywood ta tara manyan mata da maza daga kabilu daban-daban
  • A wannan zauren mun zakulo maku wasu manyan jarumai 10 da asalinsu ba Hausawa bane

Jihar Kano - Masana'antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood ita ce ta daya a bangaren nishadi a yankin arewacin kasar, kuma ta samu karbuwa sosai a wajen al'umman yankin.

Hakazalika dandalin Kannywood na dauke da manyan jarumai maza da mata wadanda ake ji da su kuma suke taka rawar gani wajen wakiltar al'adun arewa.

Sai dai kuma akwai wasu jaruman da asalinsu ba Hausawa bane amma da wuya mutum ya san da hakan musamman yadda suke magana da tsantsar hausa tamkar yarensu.

A wannan zauren, Legit Hausa ta zakulo maku wasu jarumai 10 da asalinsu ba Hausawa bane.

Read also

'Yan bindiga sun bi gida-gida a Katsina, sun hallaka mutane tare da kone dukiyoyi

1. Ummi Zeezee

Masana’antar shirya fina-finai: Jerin jaruman Kannywood 10 da asalinsu ba Hausawa bane
Masana’antar shirya fina-finai: Jerin jaruman Kannywood 10 da asalinsu ba Hausawa bane Hoto: ummizeezee
Source: Instagram

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ummi Zeezee tsohuwar jarumar masana'antar Kannywood ta kasance asalinta yar Maiduguri ce, iyayenta ba Hausawa bane domin mahaifiyarta yar kabilar Kanuri ce yayin da mahaifinta kuma ya kasance dan Shuwa Arab.

2. Rahama MK

Masana’antar shirya fina-finai: Jerin jaruman Kannywood 10 da asalinsu ba Hausawa bane
Masana’antar shirya fina-finai: Jerin jaruman Kannywood 10 da asalinsu ba Hausawa bane Hoto: dimokaradiyya.com.ng
Source: UGC

Jaruma Rahama jaruma ce wacce ta saba fitowa a cikin shiri mai dogon zango inda aka fi saninta da Hajiya Rabi Bawa mai kada, ita ma asalinta ba Bahaushiya bace Bayarbiya ce.

3. Maryam Gidado

Masana’antar shirya fina-finai: Jerin jaruman Kannywood 10 da asalinsu ba Hausawa bane
Masana’antar shirya fina-finai: Jerin jaruman Kannywood 10 da asalinsu ba Hausawa bane Hoto: Hausaloaded.com
Source: Facebook

Shahararriyar jaruma Maryam Gidado wacce aka fi sani da Maryam Babban Yaro itama ba Bahaushiya bace domin asalinta Bafulatana ce kamar yadda ta bayyana a wata hira da aka yi da ita.

4. Hassan Giggs

Masana’antar shirya fina-finai: Jerin jaruman Kannywood 10 da asalinsu ba Hausawa bane
Masana’antar shirya fina-finai: Jerin jaruman Kannywood 10 da asalinsu ba Hausawa bane Hoto: Hausaloaded.com
Source: UGC

Fitaccen darakta wanda aka jima ana damawa da shi a masana'antar ta shirya fina-finai, Hassan Giggs shima ba Bahaushe bane, asalinsa Bayarabe ne.

5. Halima Atete

Read also

Da Duminsa: Dalibai sunyi barazanar tsayar da harkoki cak a Zaria saboda sace ma'aikatan kananan hukumomi 13

Masana’antar shirya fina-finai: Jerin jaruman Kannywood 10 da asalinsu ba Hausawa bane
Masana’antar shirya fina-finai: Jerin jaruman Kannywood 10 da asalinsu ba Hausawa bane Hoto: Hausaloaded.com
Source: UGC

Halima Atete ma tana daya daga cikin manyan jaruman Kannywood mata da ake damawa da su a yanzu, ta kasance haifarfiyar yar jihar Borno daga kabilar Barebari.

6. Aina'u Ade

Masana’antar shirya fina-finai: Jerin jaruman Kannywood 10 da asalinsu ba Hausawa bane
Masana’antar shirya fina-finai: Jerin jaruman Kannywood 10 da asalinsu ba Hausawa bane Hoto: BBC.com
Source: UGC

Jaruma Aina'u Ade ta shafe tsawon shekaru ana damawa da ita masana'antar ta Kannywood, ita ma kuma asalinta Bayarbiya ce.

7. Amina Amal

Masana’antar shirya fina-finai: Jerin jaruman Kannywood 10 da asalinsu ba Hausawa bane
Masana’antar shirya fina-finai: Jerin jaruman Kannywood 10 da asalinsu ba Hausawa bane Hoto: guardian.ng
Source: UGC

Jarumar wacce ta fito a cikin fina-finan masana'antar da dama ta kasance asalinta Bafulatanar kasar Kamaru ce.

Rahotanni sun bayyana cewa a lokacin da ta shigo kasar domin fara harkar fim ko Hausa bata ji. Ta kwashe akalla shekara daya tana koyan Hausa kafin aka fara saka ta a fim.

8. Sani Musa Danja

Masana’antar shirya fina-finai: Jerin jaruman Kannywood 10 da asalinsu ba Hausawa bane
Masana’antar shirya fina-finai: Jerin jaruman Kannywood 10 da asalinsu ba Hausawa bane Hoto: agogoayonews.com
Source: UGC

Jarumi Sani Danja ya kasance tsohon jarumin masana'antar wanda ya ga jiya ya kuma ga yau, sannan da shi a ka kai masana'antar zuwa matsayin da take kai a yanzu.

Ba lallai ne mutum ya fahimci cewa asalin Sani Danja ba Bahaushe bane idan yana Hausa, sai dai kuma asalinsa Bayarabe ne.

Read also

Da duminsa: Yan bindiga sun kaiwa tsohon Soja AVM Maisaka hari gidansa dake Rigasa, sun hallakashi

9. Maryam Waziri

Masana’antar shirya fina-finai: Jerin jaruman Kannywood 10 da asalinsu ba Hausawa bane
Masana’antar shirya fina-finai: Jerin jaruman Kannywood 10 da asalinsu ba Hausawa bane Hoto: thrillng.com
Source: UGC

Tauraruwar jarumar na haskawa a cikin shiri mai dogon zango na tashar arewa 24 wato 'Labarina' haifaffiyar yar garin Gombe ce ta kuma kasance Batangaliya.

10. Mansurah Isa

Masana’antar shirya fina-finai: Jerin jaruman Kannywood 10 da asalinsu ba Hausawa bane
Masana’antar shirya fina-finai: Jerin jaruman Kannywood 10 da asalinsu ba Hausawa bane Hoto: mansurah_isah
Source: Instagram

Mansurah wacce itama ta kasance tsohuwar jaruma a masana'antar shirya fina-finan na Hausa asalinta ba Bahaushiya bace, Bayarbiya ce.

Jaruma Rahama MK, matar gwamna a fim din Kwana Casa'in ta yi auren sirri

A wani labarin, mun ji cewa ana tsaka da more shiri mai dogon zango na Kwana Casa’in sai aka wayi gari da batun auren sirri da wata jarumar fim din ta yi.

Jaridar Dimokardiyya ta ruwaito cewa, Rahama MK, wacce ta fito a matsayin matar Gwamna Bawa Mai Kada ta yi auren ta a ranar Asabar 6 ga watan Nuwamba.

Rahotanni sun nuna yadda aka yi shagalin bikin a gidan su da ke cikin garin Kano cike da sirri don ba kowa ya sani ba.

Read also

Yan ta'addan Boko Haram 17,000 suka mika wuya kawo yanzu, Kwamdanda Operation Hadin Kai

Source: Legit

Online view pixel