So makaho: Matashi ya fada soyayyar 'yar fim da ta girme shi, ya daina cin abinci saboda begenta

So makaho: Matashi ya fada soyayyar 'yar fim da ta girme shi, ya daina cin abinci saboda begenta

  • Jama'a sun tofa albarkacin bakunansu a shafukan soshiyal midiya bayan wani matashi ya bayyana irin soyayyar da yake yi wa fitacciyar jarumar Kannywood, Hadiza Muhammad
  • Matashin dai ya bayyana cewa baya iya cin abinci saboda begenta
  • Hadizan Saima dai ta girma wannan matashi domin wasu na ganin za ta iya haifarsa ma

Wani saurayi ya janyo cece-kuce a shafukan soshiyal midiya bayan ya bayyana irin soyayyar da yake yi wa fitacciyar jarumar nan ta Kannywood, Hadiza Muhammad wacce aka fi sani da Hadizan Saima.

Saurayin mai suna Farouq Abdullahi Tukuntawa ya aike da sakon soyayya zuwa ga jarumar a shafinsa na Facebook, inda ya bayyana cewa ya gagara cin abinci saboda begenta.

So makaho: Matashi ya fada soyayyar 'yar fim da ta girme shi, ya daina cin abinci saboda begenta
So makaho: Matashi ya fada soyayyar 'yar fim da ta girme shi, ya daina cin abinci saboda begenta Hoto: Farouq Abdullahi Tukuntawa
Asali: Facebook

Tukuntawa ya kuma roke ta da ta taimaka ta ceto rayuwar shi daga kogin soyayyar da ya dade da fadawa ciki.

Kara karanta wannan

Iyorchia Ayu: Muhimman abubuwa 3 game da sabon shugaban PDP da zai firgita APC kafin 2023

Ga wani bangare na sakon da ya rubuta a shafin nasa:

"Hajiya hadiza hakika na Dade ina rokon Allah madaukakin Sarki ya nuna min kwatankwachin wannan rana kafin na koma gareshi
"Ranar da zan furta miki abun da ya Dade azuciya ta koda zaki dauki hakan a matsayin shirme, zan yi farinciki da hakan domin nasan nayiwa zuciya ta babban gata domin na fitar mata da ciwon da ya Dade yana dawainiya da ita."

Ga cikakken sakon da ya wallafa a shafin nasa a kasa:

Legit.ng Hausa ta tattaro wasu daga cikin martanin da mutane suka yi a kan wannan lamari.

Sada Bin Suleiman Usman ya ce:

"Iska fa ta kaɗa."

Abdulmutallib Hamza Kibiya ya yi martani:

"Kai Yaushe ka kwato daga Dawanau?"

Kara karanta wannan

'Yan Najeriya sun manta Allah: Buhari ya bayyana mafita ga matsalolin Najeriya

Yusuf Abdulkadir ya ce:

"Bari sanyin nan ya wuce muga alkiblar ka"

Alhassan Yusha'u Kwalam ya ce:

"Ku kyaleshi sanyi ne"

Bin Imam Dandago ya yi maryani:

"Farouq Abdullahi Tukuntawa barka da cire tsoro... Lallai kayi abinda ya dace saura nima akwai wata a birnin Abuja ina matukar sonta"

Ya kamata na sassauta mishi, Jaruma Mansurah Isa ta sake magana kan tsohon mijinta Sani Danja

A gefe guda, jaruma Mansurah Isah, ta bayyana cewa har yanzun akwai kyakkyawar mu'amala tsakaninta da tsohon mijinta, Sani Musa Danja.

A wani rubutu da ta yi a shafinta na dandalin sada zumunta Instagram, Jaruma a masana'antar Kannywood, Mansurah Isa ta saki wasu hotunanta tare da tsohon mijinta, inda ta yi wasu kalamai a kansa.

Masurah ta rubuta cewa ya kamata ta buɗe tsohon mijin nata, Jarumi a Kannywood, Sani Danja, domin ya ga abinda ta buga a kansa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel