Ya kamata na sassauta mishi, Jaruma Mansurah Isa ta sake magana kan tsohon mijinta Sani Danja

Ya kamata na sassauta mishi, Jaruma Mansurah Isa ta sake magana kan tsohon mijinta Sani Danja

  • Jaruma Mansurah Isah ta yi wani rubutu a kan tsohon mijinta, Sani Musa Danja, tare da sakin wasu sabbin hotunanta tare da shi
  • Jarumar ta nuna cewa tana da kyakkyawar alaƙa tsakaninta da shi, kuma ta yi wasu kalamai na barkwanci akan Jarumin
  • Tuni dai masoyan ta suka fara tofa albarkacin bakinsu a kan sabon rubutun, inda mafi yawa suke rokonta da su sasanta kan su

Kano - Jaruma Mansurah Isah, ta bayyana cewa har yanzun akwai kyakkyawar mu'amala tsakaninta da tsohon mijinta, Sani Musa Danja.

A wani rubutu da ta yi a shafinta na dandalin sada zumunta Instagram, Jaruma a masana'antar Kannywood, Mansurah Isa ta saki wasu hotunanta tare da tsohon mijinta, inda ta yi wasu kalamai a kansa.

Masurah Isa da Sani Danja
Ya kamata na sassauta mishi, Jaruma Mansurah Isa ta sake magana kan tsohon mijinta Sani Danja Hoto: @Mansurah_Isah
Source: Instagram

Masurah ta rubuta cewa ya kamata ta buɗe tsohon mijin nata, Jarumi a Kannywood, Sani Danja, domin ya ga abinda ta buga a kansa.

Read also

Karin bayani: Sabuwar dirama ya yin da fusatattun matasa suka mamaye majalisar dokokin jihar Filato

Masurah Isah tace:

"Eyyah, Ɗan bawan Allah, shin murmushi yake yi kuwa? ku taimaka ku taya ni dibawa dan allah."

Ya kamata in buɗe shi - Mansurah

Ga dukkan alamu tun bayan rabuwar jaruman biyu, basu mu'amala a kafar sada zumunta.

Mansurah tace:

"Bai kamata wanna kwalliya ta tafi a banza ba, ina tunanin ya dace in sassauta masa na buɗe shi ko zai ga wannan rubutun."

Hotunan da jarumar ta saki

Mansura da Sani Danja
Ya kamata na sassauta mishi, Jaruma Mansurah Isa ta sake magana kan tsohon mijinta Sani Danja Hoto: @Mansurah_isah
Source: Instagram

Masurah da Danja
Ya kamata na sassauta mishi, Jaruma Mansurah Isa ta sake magana kan tsohon mijinta Sani Danja Hoto: Mansurah_Isah
Source: Instagram

Abinda mutane ke cewa:

Abdoul_Abu_Ammar yace:

"Wannan shine ake kira soyayyar da bata taɓa dusashewa, wallahi har na yi wa Sani Danja kewar rashin mace. Dan Allah ku sasanta kan ku."

Saada_Wakkala tace:

"Daman duk mai bakaken maganganu akan masoya ƙarshensa zai sha kunya, Allah ya kara haɗa kanku."

Umar Idris Galadima yace:

Read also

Ko ta wane hali zan nemi kujerar shugaban ƙasa a 2023, Tsohon shugaban majalisar dattijai

"Wallahi tsohon mijinki yaƙi dariya ne kawai, ya kamata ku warware abinda ke tsakaninku, daman aure ya gaji haka ba'a samun yadda ake so 100%."

A wani labarin kuma Sabbin zafafan Hotunan Jaruma Rahama Sadau a wurin daukar fim a Bollywood Indiya

Jaruma Rahama Sadau ta sake ɗaukar sabbin hotuna a wurin ɗaukar shirin fim a Bollywood ta ƙasar Indiya.

Tun a baya dai Sadau ta buga hotuna a dandalinta na sada zumunta, inda tace tana aikin shirin fim da masana'antar Bollywood.

Source: Legit.ng

Online view pixel