Ministan wutar lantarki na Najeriya, Adebayo Adelabu ya mika takardar murabus daga mukaminsa domin maida hankali kan burinsa na zama gwamna a jihar Oyo.
Ministan wutar lantarki na Najeriya, Adebayo Adelabu ya mika takardar murabus daga mukaminsa domin maida hankali kan burinsa na zama gwamna a jihar Oyo.
Shugaban hukumar leken asirin Isra'ila ta Mossad, David Barnea ya yi magana kan babban jami'in leken asirinsu da ya kira da Mem da ya rasu. Ya taimaka a yaki da Iran
Wasu 'yan bindiga dauke da makamai da ba a san ko su wanene ba sun hallaka dan takarar shugaban kasa a kasar Mozambique. Sun kuma hallaka lauyan 'yan adawa.
Majalisar dattawan Kenya ta kada kuri'ar tsige mataimakin shugaban kasar, Rigathi Gachagua kan cin hanci da rashawa da wasu tuhume tuhume 10 da ya musanta.
Bankin duniya ya ba Tinubu shara kan kar ya kuskura ya dawo da tallafin man fetur da farfado da darajar Naira wanda su ne tsare tsaren shugaba Bola Tinubu.
Kasar Birtaniya ta fitar da sanarwa kan neman raba Najeriya da yan a ware na kasar Yarabawa suka yi. Gwamnatin tarayya ce ta nemi Birtaniya ta yi bayani kan lamarin.
An harbi tsohon ministan jihar Maharashtra ba adadia kirji a wajen ofishin dansa a Mumbai wanda ya yi silar mutuwarsa, a cewar kafafen yada labarai na Indiya.
Tsohuwar Ministar harkokin mata ta tafka babban rashin ɗanta inda Muhammadu Buhari ya tura tawagar tsofaffin Ministocinsa 10 domin yi mata ta'azziya.
Wani matukin jirgin saman Turkiyya ya mutu bayan ya yanke jiki a cikin jirgin a lokacin da yake tuki, lamarin da ya sa jirgin ya yi saukar gaggawa a birnin New York.
A wannan rahoton za ku ji yadda kungiyar fafutuka ta Hezbollah ta bayyana cewa ana kara samun nasarori kan sojojin Isra’ila da ke kokarin kutsawa Lebanon.
Da alama kungiyar fafutuka ta Hezbollah da ke Lebanon ta gaji da yadda Isra'ila ke taka ta wajen kai hare-hare Lebanon da sauran wuraren da ke da alaka da ita.
Labaran duniya
Samu kari