Hanyoyi biyar da matan da mazajen su suke cin zarafin su zasu bi domin kare kansu

Hanyoyi biyar da matan da mazajen su suke cin zarafin su zasu bi domin kare kansu

- Albarkacin makon yaki da cin zarafin mata da majalisar dinkin duniya ta ware, mata masu fafutukar neman yancin mata sun tofa tsokacinsu

- Akwai matakai da ya kamata mace ta bi don kwato hakkinta daga wajen namiji mai dukan ta

- Wasu matan kan jure duka da cin zarafi daga miji saboda basu so a kirasu da zawarawa, wanda ba a kansu aka fara ba

Albarkacin makon yaki da cin zarafin mata da majalisar din kin duniya ta ware, mata masu rajin kare hakkin wadanda ake cin zarafi a duniya sun bada shawarwari kan yadda ya kamata a bullo wa al’amarin.

Jaridar BBC Hausa ta samu zantawa da Zainab M Lawal, mai fafutukar kare hakkin mata a Najeriya. Zainab ta ba mata shawarwarin matakai biyar da yakamata su bi don shawo kan matsalar.

Ga matakan daya bayan daya: “Da farko dai macen da ake cin zarafi ta sanar da iyayen mijin. Idan basu dauki mataki ba, zata iya fada wa iyayenta ko waliyyanta. Idan iyayen nata basu dauki mataki ba, saboda wasu iyayen zasu ce ta je ta cigaba da hakuri, auren duk hakuri ne. Zata iya zuwa wajen ‘yan sanda ko kotu don neman hakkinta.

KU KARANTA: To fah: Ban saci sisin kobo na jama'a ba, duk arzikin da nake da shi gumi na ne ya nemo mini - Saraki

“Idan su ma ‘yan sandan basu dauki mataki ba ko kotun, zata iya neman lauyoyi masu zaman kansu ko kungiyoyi masu zaman kansu. Akwai kungiyoyi masu rajin lkare hakkin mata.”

Mata na da daraja da kuma kima. Babu dacewa a ce mace ta zauna ana dukanta tare da cin zarafinta. Mace zata iya komawa gidansu. Wasu matan na tsoron yin haka ne saboda kada a kirasu da zawarawa.

Wannan Kalmar ta zarwarci ba kanki aka fara ba, kuma ba kanki za a kare ba. Don haka akwai bukatar mata su tashi tsaye don kare hakkin kansu da kansu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel