ICC: Kotun Duniya Na Neman Firaminstan Isra’ila Ruwa a Jallo Kan Kashe Falasdinawa

ICC: Kotun Duniya Na Neman Firaminstan Isra’ila Ruwa a Jallo Kan Kashe Falasdinawa

  • Babbar kotun hukunta masu manyan laifuffuka ta duniya (ICC) ta bukaci kama Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu
  • Ana zargin Benjamin Netanyahu da wasu jami'ansa ne a kan laifin kashe fararen hula a yankin Gaza a tsawon shekaru
  • Kotun ta bayyana sauran mutanen da take nema ruwa a jallo kan samunsu da hannun a kisan kiyashin da aka yi wa Falasɗinawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Kotun hukunta manyan laifuffuka ta duniya (ICC) ta sanya Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu cikin wadanda take nema ruwa a jallo.

Benjamin
Kotu ta bukaci kama firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu kan lafuffukan yaki. Hoto: @netanyahu
Asali: Twitter

Kotun duniyar ta bukaci kama Benjamin Netanyahu ne bisa zarginsa da aikata ayyukan ta'addanci a zirin Gaza a Falasdin.

Kara karanta wannan

Abin da muka sani game da hatsarin jirgin sama da ya kashe shugaban Iran

Rahoton BBC ya tabbatar da cewa mai gabatar da kara na kotun ne ya bukaci a kama Firaministan Isra'ila tare da wasu mutane.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wadanda ICC ke nema ruwa a jallo

Kotun ta bukaci a kamo mutane da suke da hannu kan halakar da rayukan fararen hula a rikicin da aka shafe shekaru ana yi cikinsu har da Benjamin Netanyahu.

Sauran mutanen sun hada da shugaban Hamaz, Yahaya Sinwar da ministan tsaron Isra'ila, Yoav Gallant, a cewar rahoton Al-Jazeera.

Wani laifi ICC ta ke zargin su?

Kotun ta ce akwai dalilai gamsassu da ke nuna cewa mutane sun aikata laifuffukan yaki a Gaza tun daga 7 ga watan Oktobar 2023 zuwa yau.

Ta kara da cewa ta binciki ayyukan ta'addanci da Isra'ila ta aiwatar a Gaza na tsawon shekaru uku da kuma ayyukan kungiyar Hamaz wanda hakan ne yasa ta ke neman su ruwa a jallo.

Kara karanta wannan

Harin masallacin Kano ya haifar da marayu da Zawarawa da dama

Yaushe ICC za ta kama Netanyahu?

A halin yanzu dai babban mai gabatar da kara na kotun ne ya ba da umurnin saboda haka za a jira hukuncin alkalan kotun kafin zartar da umurnin.

Ana sa ran alkalan za su tattauna kan lamarin ne kafin yanke hukunci cikin makonni ko kuma watanni gwargwadon yadda ya sawwaka.

Isra'ila za ta kori Al-Jazeera

A wani rahoton, kun ji cewa yayin da ake ci gaba gumurzu a Isra'ila, gwamnatin kasar ta shirya rufe gidan talabijin na Aljazeera a ƙasar.

Fira Ministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu shi ya tabbatar da haka inda ya ce za su kwace kayan aikinsu a kasar bisa zargin ruruta wutar rikicin da goyon bayan Hamas.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Online view pixel