An Nufi Fadar Shugaban Kasa Tchiani da kai Hare Hare a Nijar

An Nufi Fadar Shugaban Kasa Tchiani da kai Hare Hare a Nijar

  • An samu rahotannin karar harbe-harbe da fashe-fashe a wasu sassan birnin Yamai, babban birnin Nijar, da sanyin safiyar Asabar
  • Wata majiyar tsaro ta ce wasu ‘yan ta’adda sun kai hari filin jirgin saman Diori Hamani da kokarin kutsa kai yankin da ke kewaye da fadar shugaban kasa
  • Wata jami’ar tsaro ta ce jami’an tsaro sun kaddamar da samame tare da fatattakar maharan, yayin da wasu daga cikinsu suka tsere

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Yamai – An samu karar harbe-harbe mai tsanani da fashe-fashe a wasu sassan Yamai, babban birnin Nijar, da sanyin safiyar Asabar, lamarin da ya haifar da tashin hankali a birnin.

Wasu shaidun gani da ido biyu sun tabbatar da jin karar harbe-harbe da fashe-fashe, sai dai ba a bayyana musabbabin lamarin nan take ba.

Kara karanta wannan

Yan sanda sun shammaci ƴan bindiga suna shirin satar kaya a tirela, sun kashe 17

Abdourahamane Tchiani
Shugaban kasar Nijar, Abdourahamane Tchiani. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Harin ya shafi filin jirgi

Wata majiyar tsaro ta shaida wa Reuters cewa wasu ‘yan ta’adda sun kai hari filin jirgin saman Diori Hamani na kasa da kasa da ke Yamai, tare da kokarin kutsa kai cikin yankin da ke kewaye da fadar shugaban kasa.

Wani mazaunin birnin ya shaida cewa an ji karar harbe-harbe mai tsanani da fashe-fashe a Base 101, wani babban sansanin soji da ke Yamai.

Bana Wagana Ibrahim, mamba a Ofishin Majalisar Shawara ta Nijar kuma mataimaki a Majalisar Tarayyar Kasashen Sahel (AES), ya ce maharan sun kai hari sansanin Base 101.

Ya sanar da cewa:

“Wani sabon hari na matsorata kan Base 101, kuma a wannan karon ma jami’an tsaronmu da sojojinmu sun tabbatar da cewa… lamarin yana karkashin iko,”

An kaddamar da bincike

Wata majiya ta biyu daga jami’an tsaro ta ce hukumomi sun fara gudanar da samame da bincike domin gano sauran maharan.

Kara karanta wannan

Yan takara 3 da suka sha alwashin dawo da tallafin fetur idan aka zabe su

Al Jazeera ta walllafa cewa majiyar ta ce an “kawar da” wasu daga cikin maharan, yayin da wasu kuma suka tsere daga wurin.

Wani shaida ya ce karar harbe-harben ta kasance mai tsanani kuma ba ta yankewa a yankin da ke kusa da fadar shugaban kasa.

Wani shaidan gani da ido na farko ya ce an sake jin karar harbe-harbe a kusa da filin jirgin saman kasa da kasa na Yamai da misalin karfe 2:13 na dare.

Abdourahamane Tchiani a Nijar
Shugaban Nijar, Abdourahamane Tchiani, da wasu sojoji. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Hotunan bidiyo da aka wallafa a kafafen sada zumunta sun nuna motocin sulke da aka girke domin karfafa tsaron yankunan da ke kusa da filin jirgin.

Ana shirin ceto jama'a a Neja

A wani labarin, mun ruwaito cewa jami’an tsaro da suka hada da sojoji, ‘yan sanda da jami’an Hukumar DSS sun shiga Karamar Hukumar Borgu ta Jihar Neja domin ceto mutane.

Matakin ya biyo bayan umarnin Shugaba Bola Tinubu ga jami’an tsaro da su shiga yankin, su tabbatar da tsaron al’ummomin da abin ya shafa tare da ceto mutanen da aka sace.

Yayin da ‘yan sanda suka ce adadin mutanen da aka sace ya kai tsakanin 155 zuwa 164, ‘yan ta’addan sun yi ikirarin cewa suna rike da mutane sama da 500.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng