An samar wa sojojin da ke yakar 'yan Boko Haram jirgin yawo lokacin hutu
- Rundunar sojin Najeriya ta samar da jirgin jigila ga sojojin Najeriya da ke kan aiki a Maiduguri
- Rundunar ta bayyana manufar samar da jirgin da cewa, zai taimaka wajen tabbatar da jin dadin sojoji
- An lura cewa, jami'an na tafiya zuwa wuri mai nisa domin zuwa hutu yayin da suke kan izinin ficewa na wucin gadi
Borno - Rundunar Sojin Najeriya ta bayyana cewa za a samar da jirgin saman zirga-zirga ga sojoji da manyan jami'ai a fagen daga wadanda aka ba izinin ficewa na wucin gadi da nufin zuwa ganin danginsu yayin da suke kan aiki.
Jaridar TheCable ta ba da rahoton cewa izinin ficewar, a yaren sojoji, izini ne na barin sashin aiki na dan wani lokaci.
Legit.ng ta tattaro cewa mafi yawan sojoji da jami'ai da aka tura daga sassa daban-daban na kasar zuwa rundunar Operation Hadin Kai a arewa maso gabas suna tafiya daruruwan kilomita lokacin da suke kan izinin ficewa na wucin gadi domin ganin danginsu.
Onyema Nwachukwu, mai magana da yawun rundunar, ya bayyana a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, 10 ga watan Agusta, cewa babban hafsan sojin kasa, Faruk Yahaya, ya kaddamar da jirgin jigilar jindadin sojoji a sansanin sojojin sama dake Maiduguri, jihar Borno.
Wannan ya faru ne jiya Litinin, 9 ga watan Agustan 2021.
Yadda aka tsara tafiyar da jigilar jirgin
Ya ce ci gaban wani bangare ne na kokarin babban hafsun soji na kula da jin dadin sojojin da ke son zuwa gida daga sansanoninsu na ayyukan zuwa wasu sassan kasar.
Nwachukwu ya kara da cewa jirgin mai suna Nigerian Air Force Charlie-130, babban hafsan sojin sama ne, Isiaka Amao ne ya bayar da shi ga sojojin.
Yahaya ya bayyana cewa jirgin zai kasance cikin jigila sau biyu a wata don daddale hutun makonni biyu na izinin hutu a sansanonin aiki, ya kara da cewa za a ba wa ma’aikatan da suka tafi izinin hutun wucin gadi na makonni biyu.
Shugaban hafsun soji ya bukaci jami'ai su yi adalci wajen daukar sabbin sojoji
A wani labarin, Faruk Yahaya, shugaban hafsan sojojin Najeriya, ya yi kira ga hafsoshi da ma’aikatan da ke gudanar da aikin tantance zababbun ma’aikatan rukuni na 81 na shiga aikin sojojin Najeriya da su kasance masu adalci da gaskiya.
Yahaya ya ba da umarnin ne a ranar Asabar, lokacin da ya ziyarci cibiyar horar da sojojin Najeriya da ke sansanin Falgore a jihar Kano, inda ake gudanar da aikin tantancewar.
Daraktan hulda da jama’a na rundunar Onyema Nwachukwu ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa a ranar Asabar, 7 ga watan Agusta a Abuja, The Cable ta ruwaito.
Asali: Legit.ng