Ana tsakiyar Musayar Wuta, Kasar Iran Ta Sake Ruguza Lissafin Amurka da Isra'ila

Ana tsakiyar Musayar Wuta, Kasar Iran Ta Sake Ruguza Lissafin Amurka da Isra'ila

  • Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta sake fitowa ta karyata ikirarin cewa an fara tattaunar sulhu da tsagaita wuta tsakaninta da Amurka/Isra'ila
  • Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Iran, Esmaeil Bagaei, ya nanata cewa kasar ba ta kai ga komawa teburin tattaunawa ba
  • A yan kwanakin nan, Gwamnatin Amurka ta sha cewa tattaunawar tsagaita wuta tsakaninta da Iran na ci gaba da gudana kuma an samu ci gaba

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Iran - Gwamnatin Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta sake nanata cewa har yanzu ba ta shiga wata tattaunawa da nufin kawo karshen yakin da ke gudana a Gabas ta Tsakiya.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran, Esmaeil Bagaei, ya bayyana cewa kasar ba ta shiga wata tattaunawa da Amurka ko Isra'ila ba tun bayan fara yakin da ake yi da ita.

Kara karanta wannan

Tirkashi: Amurka ta sha alwashi, ta fadi abin da ba za ta bari Iran ta mallaka ba

Jagroan imIran.
Jagoran addini na kasar musulunci ta Iran, Mojtaba Khamenei Hoto: Jafara Hamid
Source: Getty Images

Da gaske Iran ta koma teburin tattaunawa?

Rahoton tashar Al-Jazeera ya nuna cewa Bagaei ya bayyana haka ne a wasu sakonni da ya fitar yau Litinin, 30 ga watan Maris, 2026.

"Ba mu shiga wata tattaunawa da Amurka ba a cikin kwanaki 31 da muka yi muna gwabzawa," in ji shi.

Sai dai ya bayyana cewa abin da ya faru shi ne Amurka ta gabatar da bukatar tattaunawa tare da wasu shawarwari, wadanda suka iso hannun Iran ta hannun wasu kasashe da suka shiga tsakiya tare daciki har da Pakistan.

Matsayar Iran kan batun tsagaita wuta

Bagaei ya jaddada cewa matsayar Iran kan tsagaita wuta ba ta sauya ba tun bayan fara yakin a ranar 28 ga watan Fabrairu, 2026.

“Matsayarmu a fili take. A halin yanzu da Amurka ke ci gaba da kai hare-hare da karfi, dukkan kokarinmu yana karkata ne wajen kare mutuncin kasar Iran," in ji shi.

Kara karanta wannan

Pakistan ta faɗi halin da ake ciki a kokarin sulhunta Iran da Amurka

Ya kuma zargi Amurka da cewa ta ci amana tare da yi wa tsarin diflomasiyya zagon kasa sau biyu cikin kasa da shekara guda, kmaar yadda Vanguard ta wallafa a rahoton ta.

Shugaban Amurka.
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump a fadar White House Hoto: Roberto Schmidt
Source: Getty Images

Kasar Iran ta zargi Amurka da cin amana

A cewarsa, daya daga cikin wadannan lokuta shi ne yakin kwanaki 12 da aka yi a watan Yunin 2025, wanda ya fara da hare-haren Amurka da Isra’ila kan cibiyoyin soja da na nukiliya na Iran yayin da ake cikin tattaunawa.

Wannan bayani na Iran na nuna cewa har yanzu babu wani ci gaba a bangaren sulhu, yayin da rikicin ke ci gaba da tsananta tsakanin bangarorin biyu duk da Amurka ta ce an fara tattaunawa.

Iran za ta samun damar kera nukiliya?

A wani labarin, kun ji cewa kasar Amurka ta bayyana cewa ba za ta bari Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta mallaki makamakin nukiliya ba.

Ministan harkokin wajen Amurka, Marco Rubio, ya yi ikirarin cewa gwamnatin Iran na son mallakar makaman nukiliya ne domin yi wa duniya barazana da tsoratarwa, amma ba za su taɓa barin hakan ta faru ba.

Ya bayyana cewa dole ne Iran ta ɗauki kwararan matakai wajen watsi da shirinta na nukiliya da kowane irin buri na mallakar makaman nukiliya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262