Trump Ya Yi Barazanar Kai wa Iran Harin da 'Ba a Taba Ganin Irin Sa ba'

Trump Ya Yi Barazanar Kai wa Iran Harin da 'Ba a Taba Ganin Irin Sa ba'

  • Shugaban kasar Amurka, Donald J. Trump, ya yi gargadi ga Iran kan yiwuwar dasa nakiyoyi a mashigar ruwa ta Hormuz
  • Trump ya ce idan an dasa nakiyoyin kuma ba a cire su nan take ba, Amurka za ta dauki matakin soja mai tsauri
  • Ya kuma yi barazanar cewa duk wani jirgin ruwa da zai yi kokarin dasa nakiyoyi a yankin zai fuskanci mummunan hari

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

USA – Shugaban kasar Amurka, Donald J. Trump, ya yi gargadi mai tsauri ga gwamnatin Iran dangane da yiwuwar dasa nakiyoyi a mashigar ruwa ta Hormuz.

Wannan ya biyo bayan rahotannin da aka samu cewa akwai yiwuwar Iran na dasa nakiyoyi a wannan muhimmin wuri da jiragen ruwa ke bi domin safarar man fetur da sauran kayayyaki a duniya.

Kara karanta wannan

Shugaba Edogan ya yi gargadi da ya hango gagarumar matsala a yakin Iran da Amurka

Trump ya kuma wani gargadin ga Iran
Shugaban Amurka Donald J Trump a yayin wani taro Hoto: Getty
Source: Twitter

Fox News ta wallafa cewa Shugaban ya sanar da cewa idan har Iran ta dasa nakiyoyi a mashigar ruwan, ya kamata ta cire su nan take.

Trump ya sake gargadin Iran

CBS News ta wallafa cewa duk da haka, Trump ya ce har yanzu babu rahotannin da ke tabbatar da cewa an dasa nakiyoyin.

Sai dai Shugaban na Amurka ya jaddada cewa idan aka tabbatar da cewa an dasa nakiyoyi kuma ba a cire su cikin gaggawa ba, Amurka za ta dauki matakin soja mai tsauri wanda ba a taba ganin irinsa ba.

Trump ya kara da cewa idan Iran ta cire duk wani abu da aka sanya a yankin, hakan zai zama babban mataki na gyara al’amura da rage tashin hankali.

Trump ya ce za su kai hari kan jiragen Iran
Shugaban Iran, Masoud Pezeshkian a tsakiya tare da manyan kasa a wani taro Hoto: Getty
Source: Getty Images

Mashigar ruwan Hormuz na daya daga cikin wuraren da suka fi muhimmanci a harkar kasuwancin man fetur a duniya.

Dalilin da ya sa wurin ke da muhimmanci shi ne saboda yawancin jiragen dakon mai daga kasashen Gabas ta Tsakiya na bi ta wannan hanya zuwa sauran sassan duniya.

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: Sojojin Iran sun ja kunnen Trump kan neman tsayar da yaki

Trump ya ce Amurka na sa ido

A cikin sakon nasa, Trump ya kuma bayyana cewa Amurka na amfani da irin fasahar soja da kuma makaman linzami da ta taba amfani da su wajen yakar masu safarar miyagun kwayoyi.

Ya ce za a yi amfani da irin wannan fasaha domin dakile duk wani jirgin ruwa ko kwale-kwale da zai yi kokarin dasa nakiyoyi a mashigar ruwan.

A cewarsa, duk wani jirgin ruwa da aka samu yana kokarin yin irin wannan aiki zai fuskanci matakin gaggawa daga sojojin Amurka.

Ya kuma yi gargadi mai tsauri ga duk wanda ke da niyyar aikata irin wannan aiki, yana mai cewa sakamakon da zai biyo baya zai kasance mai tsanani.

Trump ya sake jaddada gargadin da ya yi, yana mai cewa duk wani yunkuri na dasa nakiyoyi a mashigar ruwan Hormuz zai gamu da matakin gaggawa daga Amurka.

Isra'ila ta fara ganin sakamakon yakar Iran

A baya, mun wallafa cewa dangantakar diflomasiyya ta yi tsami tsakanin kasar Spain da Isra'ila tun bayan da aka kaddamar da hare-hare kan Iran a watan Fabrairu, 2026.

Kara karanta wannan

Amurka ta taɓo China a yaƙin Iran, ta tura gargaɗi kan rufe mashigar Hormuz

Firaministan Spain, Pedro Sanchez, wanda ya sha sukar Isra'ila kan kashe Falasdinawa a Gaza ya yi Allah wadai da yakin wanda ya ce ko kadan bai kamata ba.

A ranar Laraba, 11 ga watan Maris 2026, gwamnatin Spain ta sanar da janye jakadanta daga kasar Isra'ila wanda hakan ya nuna tabarbarewar alaka tsakanin kasashen biyu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng