'Kisan Kiristoci': An Ware Jihar da Ake So Trump Ya Kafa Sansanin Soja a Najeriya

'Kisan Kiristoci': An Ware Jihar da Ake So Trump Ya Kafa Sansanin Soja a Najeriya

  • Dr. Walid Phares ya bukaci Shugaba Donald Trump ya kafa sansanin gaggawa na soja a birnin Port Harcourt, jihar Rivers
  • Masani kan harkokin kasashen wajen ya ce hakan zai taimaka wajen hana kungiyoyin ‘yan ta'adda kashe Kiristoci a kasar
  • Phares ya ce sansanin zai taimaka wajen kai agajin jin kai ga Kiristoci da tsirarun Musulmi cikin sauri daga coci-cocin Amurka

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Amurka — A wani lamari mai ban mamaki, Dr. Walid Phares, masani kan harkokin kasashen waje, ya tsoma baki kan rikicin Donald Trump da Najeriya.

Ya bukaci shugaban Amurka Donald Trump da ya kafa sansanin soja na gaggawa a birnin Port Harcourt da ke jihar Rivers.

An shawarci Trump ya kafa sansanin soja a jihar Rivers
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump. Hoto: @realDonaldTrump
Source: Getty Images

Ana so Trump ya kafa sansani a Najeriya

Dr. Phares, wanda ke aiki a matsayin babban sakataren kungiyar TPG, ya bayyana hakan ne a shafinsa na X (Twitter) a ranar Lahadi.

Kara karanta wannan

"Abin da dole Trump ya yi kafin kawo hari Najeriya": Hadimin Tinubu ya yi bayani

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa, kafa sansanin soja cikin gaggawa a Port Harcourt zai taimaka wajen dakile hare-haren Boko Haram da sauran kungiyoyin 'yan ta'adda masu jihadi.

Ba iya dakile hare-haren Boko Haram da 'yan ta'adda masu jihadi ba, masanin ya ce hakan zai kuma kare Kiristoci da "tsirarun Musulmi" daga kisa da barazana.

“Wannan matakin zai baiwa Amurka damar aika agajin jin kai cikin gaggawa, musamman daga coci daban daban da ke Amurka,” in ji Dr. Phares.

Kalaman Trump kan Najeriya sun daga hankula

A makon da ya gabata, Shugaba Donald Trump ya ayyana Najeriya a matsayin “wulaƙantacciyar ƙasa,” saboda, a cewarsa, ba ta ba da kariya ga Kiristoci da sauran masu ƙananan addinai.

Trump ya kuma yi barazanar cewa Amurka za ta iya daukar matakin soja idan gwamnatin Najeriya ta kasa dakatar da kisan Kiristocin da ake yi.

Saboda wannan magana ta Trump, masani kan harkokin kasashen waje, Dr. Phares ya ce:

Kara karanta wannan

'Ta sama ko ta kasa,' Donald Trump ya fadi shirinsa kan kai hare hare Najeriya

“Don dakile Boko Haram da sauran kungiyoyin masu jihadi a Najeriya, da kuma hana kisan Kiristoci da barazana ga tsirarun Musulmi, ina shawartar gwamnatin Trump ta kafa sansanin soja a Port Harcourt — babban birnin yankin Biafra."
Masanin harkokin kasashen waje, Dr. Phares ya shawarci Trump ya kafa sansani a Najeriya.
Hoton shugaban kasar Amurka, Donald Trump, da masani kan harkokin waje, Dr. Phares. Hoto: @realDonaldTrump, @WalidPhares
Source: Twitter

Gargadin masana ga shugaba Trump

Sai dai, mun ruwaito cewa, gwamnatin Najeriya ta karyata ikirarin cewa ana zaluntar wata ƙungiyar addini a cikin ƙasar.

Mai magana da yawun gwamnatin Najeriya, Daniel Bwala ya ce Najeriya ƙasa ce mai ’yancin addini, kuma gwamnati na ɗaukar matakan kare kowa ba tare da nuna bambanci ba.

Amma a cewar Dr. Phares, Shugaba Trump ya riga ya umarci ma'aikatar yaƙin Amurka da ta shirya shirin kariya na musamman idan gwamnatin Najeriya ta kasa dakatar da masu jihadi.

Masana harkokin diflomasiyya dai sun yi gargadin cewa irin wannan shawarar za ta iya tayar da rikicin diflomasiyya tsakanin Amurka da Najeriya, musamman ganin Port Harcourt na cikin yankin da ba na rikici ba.

Amurka za ta fara gwajin nukiliya

A wani labarin, mun ruwaito cewa, shugaban kasa Donald Trump ya bukaci hedikwatar tsaron Amurka ta fara gwajin makaman Nukiliya nan da nan.

Kara karanta wannan

Martanin wasu manyan Arewa kan barazanar Trump ta kai farmaki Najeriya

Donald Trump ya ce Amurka za ta fara gwajin nukiliya kamar sauran ƙasashe saboda wasu na ci gaba da yin gwajin a fili, duk da yarjejeniyar da aka yi.

Sai dai wannan mataki ya jawo martani, inda wasu ke ganin cewa matakin na iya tayar da sabon rikicin nukiliya, yayin da Rasha ta ce za ta dauki mataki a kai.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com