Ghana Za Ta Taimakawa Najeriya Da Wutar Lantarki Bayan Samun Matsala A Kasar

Ghana Za Ta Taimakawa Najeriya Da Wutar Lantarki Bayan Samun Matsala A Kasar

  • Hukumar Samar da Wutar Lantarki a Ghana ta yi alkawarin taimakawa Najeriya da wutar lantarki
  • Kasar ta ce za ta taimakawa Najeriya wurin tabbatar da samun kaso 100 na karfin wutar lantarki a duniya
  • Shugaban hukumar, Henson Monney shi ya bayyana haka a jihar Legas yayin taron makamashi

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Accra, Ghana - Kasar Ghana ta shirya taimakon Najeriya da wutar lantarki ganin yadda kasar ke fama da wannan matsala.

Shugaban hukumar samar da wutar lantarki a Ghana, Henson Monney shi ya bayyana haka yayin wani taro a jihar Legas, Legit ta tattaro.

Ghana za ta taimakawa Najeriya da wutar lantarki
Ghana ta dauki aniyar taimakon Najeriya da wutar lantarki. Hoto: Horacio Villalobos/Contributor.
Asali: Getty Images

Da meye Ghana ke shirin taimakon Najeriya da shi?

Ya ce Ghana ta cika kaso 80 zuwa 85 na karfin wutar lantarki saboda tsare-tsare masu kyau.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Saura Kiris: Ministan Makamashi Ya Yi Wa Yan Najeriya Wani Muhimmin Albishir Kan Wutar Lantarki

Kasar na son taimakawa Najeriya ta samu kaso 100 na karfin wutar lantarki a duniya.

Ya ce da zarar Najeriya ta gyara matsalolin wutar lantarki a kasar, Ghana za ta fara taimaka mata da wutar.

Najeriya na fama da matsalar wutar lantarki sama da shekaru 50 wanda gwamnatoci da dama su ka gagara shawo kan matsalar

Meye dalilin taimakawa Najeriya da Ghana ke shirin yi?

Wannan na zuwa ne bayan kasar Najeriya ta samu lalacewar wutar lantarki har sau biyu a cikin mako guda, cewar Nairametrics.

An shafe shekara daya ba tare da samun irin wannan matsala ba tun lokacin mulkin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari.

Duk da matsalar wutar a kasar, Najeriya ta yanke wutar da ta ke taimakawa Jamhuriyar Nijar saboda matsalar diflomasiyya a tsakanin kasashen.

Najeriya ta dauki matakin ne bayan hambarar da Mohamed Bazoum na Jamhuriyar Nijar a ranar 26 ga watan Yuli da sojoji su ka yi.

Kara karanta wannan

Babbar Magana: An Kama a Wani Mutumi da Ake Zargi da Lalata da Ɗiyarsa, Ta Mutu a Yanayi Mai Mamaki

An dauke wutar lantarki gaba daya a Najeriya

A wani labarin, a karon farko cikin shekara daya, an dauke wutar lantarki a fadin Najeriya baki daya a safiyar Alhamis 14 ga watan Satumba.

Kamfanin samar da wutar a Najeriya (TCN) ya tabbatar da lalacewar wutar lantarki a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis 14 ga watan Satumba.

Wannan shi ne karon farko a cikin shekara daya da aka dauke wutar lantarki gaba daya a Najeriya tun bayan daukewarta a lokacin mulkin tsohon shugaban kasa, Buhari.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.