Sheikh Salih Al Fawzan: Saudiyya Ta Nada Shugaban Malamai Masu Fatawa

Sheikh Salih Al Fawzan: Saudiyya Ta Nada Shugaban Malamai Masu Fatawa

  • Gwamnatin Saudiyya ta nada Sheikh Dr Ṣāliḥ bin Fawzān Al-Fawzān a matsayin Babban Mufti na ƙasar tare da matsayin minista
  • Sheikh Al-Fawzān, wanda aka haifa a garin Ash-Shamāsiyyah a 1935, ya yi karatunsa har zuwa digirin PhD a jami’ar Imam a Saudi
  • Tarihi ya nuna cewa sabon muftin ya shahara wajen koyarwa a masallatai da makarantu, rubuce-rubuce, da bayar da fatawowin Musulunci

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Saudiyya – Gwamnatin Saudiyya ta sanar da nadin Sheikh Dr Ṣāliḥ bin Fawzān Al-Fawzān a matsayin babban Mufti na ƙasar.

Malamin ya zamo shugaban majalisar manyan malamai, da kuma shugaban hukumar binciken addini da fatawa, tare da masa karin matsayin minista.

Sheikh Saliḥ bin Fawzan Al-Fawzan
Sabon muftin Saudiyya, Sheikh Saliḥ bin Fawzan Al-Fawzan. Hoto: Inside Haramain
Source: Facebook

Shafin Inside the Haramain ya wallafa a Facebook cewa an haifi Sheikh Al-Fawzān a garin Ash-Shamāsiyyah da ke yankin Al-Qassim a shekarar 1935.

Kara karanta wannan

Duniyar Musulunci ta yi babban rashi, Mufti Haji Umer na Habasha ya rasu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tarihin karatun Sheikh Saliḥ Al-Fawzan

Sheikh Al-Fawzān ya fara karatunsa a makarantun garinsu kafin daga bisani ya tafi jami’ar Imam Muhammad bin Saud, inda ya karanci shari’ar Musulunci har zuwa digirin PhD.

Binciken da ya yi a digirinsa na farko ya mayar da hankali kan dokokin gado, yayin da bincikensa na PhD ya tattauna kan hukuncin halal da haram a abinci.

Ya yi karatu a gaban fitattun malamai irin su Sheikh Abdullah bin Hamid, Sheikh Ibrahim bin Ubayd a Buraydah, da kuma Sheikh Abdulaziz bin Baz a Riyadh.

Gwagwarmayar ilimi da koyarwa

Bayan kammala karatunsa, Sheikh Al-Fawzān ya fara aikin koyarwa a wata makaranta a Riyadh, daga bisani a Kwalejin Shari’a, kafin ya zama shugaban babban cibiyar shari’a.

A tsawon shekaru, ya horar da dubban alkalai da malamai waɗanda suka yada ilimi a faɗin ƙasar Saudiyya.

Sheikh Fawazan da Sudais
Sabon muftin Saudiyya tare da Sheikh Sudais. Hoto: Inside the Haramain
Source: Facebook

Haka kuma ya shafe shekaru yana limanci da yin wa’azi a masallacin Mutaib bin Abdulaziz da ke Riyadh, inda yake koyar da akida, fikihu, rabon gado da nahawu.

Kara karanta wannan

Kusa a APC ya ba Shugaba Tinubu shawara kan yajin aikin ASUU

Gudumuwa ga da’awa da rubuce-rubuce

Rahoton Arab News ya nuna cewa Sheikh Al-Fawzān ya shahara a duniya ta hanyar shirin radiyo na Saudiyya mai suna Noor ala al-Darb, inda yake amsa tambayoyi.

Ya rubuta littattafai da dama kamar Al-Irshad ila Saheeh al-I’tiqad, Al-Bayan li-Akhṭa’ Ba’ḍ al-Kuttab, da Al-Khuṭab al-Minbariyyah mai juzu’i huɗu, waɗanda suka zama madogara ga ɗalibai da malamai.

Haka kuma ya taimaka wajen tsara manhajojin karatun addini a makarantu domin tabbatar da ingantaccen koyarwa bisa hujja da ilimi.

Sheikh Al-Fawzan ya zama Muftin Saudi

Sheikh Dr. Ṣāliḥ Al-Fawzān ya karɓi mafi girman mukami na addini a Masarautar Saudiyya — wanda ke kula da binciken addini, bayar da fatawowi, da jagorantar majalisar manyan malamai.

Saudiyya ta masa fatan alheri da cewa:

"Allah Ya kiyaye Sheikh Dr Ṣāliḥ Al-Fawzān, ya albarkaci aikinsa, ya kuma sa iliminsa ya ci gaba da zama haske ga al’ummar Musulmi."

Kara karanta wannan

'An fi kashe Musulmi,' Hadimin Trump ya karyata zargin kisan Kiristoci a Najeriya

Muftin Saudiyya ya rasu a Riyadh

A wani rahoton, kun ji cewa a watan da ya wuce ne Allah ya karbi rayuwar shugaban malaman Saudiyya, Sheikh Abdulaziz bin Abdallah Al Sheikh.

Sheikh Al Sheikh ya rasu ne bayan shafe shekaru yana jagorantar hudubar Arafa da sauran abubuwan da suka shafi addini.

An masa jana'iza a birnin Riyadh kamar yadda addinin Musulunci ya tanada tare da kira a masa sallar gawa daga nesa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng