'An Fi Kashe Musulmi,' Hadimin Trump Ya Karyata Zargin Kisan Kiristoci a Najeriya
- Mai ba shugaba Donald Trump shawara, Massad Boulos ya ce Boko Haram da ISIS sun fi kashe Musulmai fiye da Kiristoci
- Hadimin shugaban kasar ya ce rashin tsaro a Najeriya bai shafi addini ba, domin yana shafar kowa daga kowane yanki na kasar
- Boulos ya yabawa gwamnatin shugaba Bola Tinubu bisa ƙarin matakan tsaro da suka kawo sauyi a wasu yankunan da ake rikici
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Mai ba shugaba Donald Trump shawara kan kasashen Larabawa da Afirka, Massad Boulos, ya bayyana cewa 'yan ta'adda na kashe Musulmi da Kirista.
Ya ce kungiyoyin ta’addanci kamar Boko Haram da ISIS sun kashe Musulmai da dama fiye da Kiristoci a Najeriya.

Source: Facebook
Ya yi wannan bayani ne a cikin wani bidiyo da gidan talabijin na NTA ya wallafa a shafin X, inda yake amsa tambayoyi game da zargin cin zarafi saboda addini a Najeriya.

Kara karanta wannan
'Yan bindiga sun kashe fiye da mutane 10 a sabon harin da suka kai garuruwan Filato
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Boulos ya karyata batun kashe Kiristoci
Massad Boulos ya bayyana cewa ta’addanci a Najeriya ba ya da alaƙa da addini ko kabila, domin kowa na fuskantar bala’in rashin tsaro.
A cewarsa:
“Mutane da suka san halin da ake ciki sun san cewa ta’addanci ba ya da launi, addini ko ƙabila. Boko Haram da ISIS sun fi kashe Musulmai fiye da Kiristoci.
"Mutane daga kowane bangare na ƙasar suna fuskantar wahala iri ɗaya.”
Ya ƙara da cewa duk wani asarar rai da za a yi abin bakin ciki ne, kuma bai kamata a nuna cewa ana kai hari ga wani rukuni ɗaya kawai ba.
Magana kan rikicin manoma/makiyaya
Boulos ya bayyana cewa wasu tashin-tashina da ake samu a Arewa ta Tsakiyar Najeriya tsakanin makiyaya da manoma ba rikicin addini ba ne.
Punch ta wallafa cewa ya ce:
“Akwai lamarin da ke faruwa a yankunan Arewa ta Tsakiya, inda yawancin manoma Kiristoci ne, kuma makiyaya suna bi ta wajen.
"Idan rikici ya faru, ba yana nufin ana kai wa wani addini hari ba ne.”
Boulos ya jaddada cewa irin waɗannan matsaloli sun fi danganta da rikicin filayen noma da kiwo, ba batun addini ba.
Hadimin Trump ya yabi Tinubu
Mai ba wa Trump shawara ya yaba wa gwamnatin Bola Tinubu bisa ƙoƙarin ƙarfafa tsaro, musamman a yankuna da ke fama da rikici.
Ya ce:
“Mun ga ƙarin matakan tsaro da gwamnatin Tinubu ta ɗauka kwanan nan, kuma hakan ya fara kawo sauyi. Muna maraba da waɗannan matakai, tare da fatan za a ƙara inganta su.”
Ya bayyana cewa matakan da ake ɗauka yanzu sun nuna alamun cewa gwamnati na iya rage barazanar ta’addanci da tashin hankali.

Source: Facebook
Boulos ya bukaci ƙasashen Amurka da Najeriya su ci gaba da haɗa kai wajen kawar da ta’addanci da tabbatar da zaman lafiya a dukkan yankuna.
Miji ya kashe kwarto a gidansa da dare
A wani rahoton, kun ji cewa wani mutum a karamar hukumar Ningi ya lakadawa wani da ake zargi kwarto ne duka.
Bayanai sun nuna cewa dukan da aka yi wa wanda ake zargin ya kai ga masa illa kuma ana kai shi asibiti aka tabbatar ya mutu.
Rundunar 'yan sanda ta tabbatar da cewa mijin da ya yi dukan ya gudu kuma ana cigaba da bincike domin kamo shi.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

