Trump Ya Saɓa da Neyanyahu kan Harin Ƙasar a Doha, Isra'ila Ta Yi Zazzafan Martani

Trump Ya Saɓa da Neyanyahu kan Harin Ƙasar a Doha, Isra'ila Ta Yi Zazzafan Martani

  • Kasar Isra’ila ta yi magana kan harin da ta kai a birnin Doha duk da ikirarin Shugaba Donald Trump na Amurka
  • Kasar ta kare harin da ta kai kan shugabannin Hamas a Qatar bayan sukar hakan daga Trump, wanda ya bayyana rashin amincewa
  • Jakadan Isra’ila a Majalisar Dinkin Duniya, Danny Danon, ya ce ba hari kan Qatar ba ne, hari ne kan 'yan kungiyar Hamas

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Tel Aviv, Isra'ila - Kasar Isra’ila ta yi martani bayan kai hari a birnin Doha na kasar Qatar kan shugabannin kungiyar Hamas.

Isra'ila ta kare hare-haren da ta kai kan Qatar a ranar Laraba, duk da suka daga shugaban Amurka Donald Trump.

Netanyahu da Trump sun bambanta kan harin Isra'ila a Doha
Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu da Shugaba Donald Trump. Hoto: Benjamin Netanyahu, Donald J.Trump.
Source: UGC

Rahoton CNN ya ce Shugaba Trump ya nuna rashin goyon baya kan harin inda ya ce bai da masaniya.

Kara karanta wannan

Tinubu: Sai da rajistar haraji za a yi hulda da banki a Najeriya daga 2026

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Amurka ta magantu kan harin Isra'ila a Qatar

Fadar White House ta ce Trump bai amince da harin ba, ya kuma gargadi Qatar kafin kai harin, sai dai ƙasar ta ce ba ta samu sanarwa ba.

Qatar, wadda ke da babban sansanin sojin Amurka, ta ce an sanar da ita bayan harin ya riga ya afku, inda mutane suka mutu.

Jakadan kasar Isra’ila a Majalisar Dinkin Duniya ya kare matakin, inda ya ce ba koyaushe suke aiki don Amurka ba.

Ya ƙara da cewa:

“Muna samun daidaito, suna bamu goyon baya, amma wani lokaci muna ɗaukar mataki sannan mu sanar da Amurka, hari ne kan Hamas ba kan Qatar ba."

Ya kuma tabbatar da cewa ƙasar Isra’ila ba ta adawa da ƙasashen Larabawa kamar yadda ake zato.

Harin Isra'ila a Qatar ya bar baya da kura
Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu bayan kammala taro. Hoto: Benjamin Netanyahu.
Source: Getty Images

Asarar da aka yi wa kungiyar Hamas

Hamas ta ce mutane shida sun mutu ciki har da ɗan babban mai tattaunawar sulhu, Khalil al-Hayya, yayin da manyan shugabanninta suka tsira.

Kara karanta wannan

Majalisa na barazanar hada minista da Tinubu kan 'raina' 'yan Najeriya da suka yi hadari

Qatar ta tabbatar da mutuwar jami’in tsaronta guda ɗaya, yayin da aka ce har yanzu suna jiran sakamakon aikin sojoji da aka aiwatar.

Ya ce:

“Da wuri ne a yi sharhi kan sakamakon, amma wannan shawarar ita ce ta dace.”

Rahotanni sun ce shugabannin Hamas guda shida sun kasance a wurin harin, ciki har da Khaled Meshaal, amma ba a iya samun su ba.

Qatar ta ce hare-haren sun kai ga gidajen ‘yan Hamas da ke kasar, inda aka kashe masu tsaro uku da kuma ɗan mai tattaunawar kungiyar, cewar rahoton BBC.

Hamas ta ce:

“Maƙiyi bai yi nasarar kashe ‘yan tawagar tattaunawarmu ba."

Firayim Ministan Qatar ya ce harin ya kasance a lokaci mai muhimmanci ga yankin, inda Isra’ila ta ce ta ɗauki mataki bayan harin Hamas a Urushalima.

Trump zai taimaka wa Falasɗinawa da kudi

Kun ji cewa shirin sake fasalin Gaza na gwamnatin Donald Trump ya yi nuni da yiwuwar ba wa Falasdinawa kudi domin barin yankin.

Ana tunanin kafa sababbin garuruwa masu fasahar zamani da cibiyoyin kasuwanci bayan kwashe mazauna yankin Gaza.

Kara karanta wannan

An zo wajen: Gwamnatin Tinubu ta yi magana kan lokacin fara biyan harajin fetur

Kasashen Larabawa na iya kalubalantar wannan tsari yayin da wasu suke ba da goyon baya ga wani shiri dabam na biliyoyin Daloli.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.