Hukumomin Turkiyya Sun Cafke 'Yan Jarida bisa Zana 'Hoton' Annabi Muhammad SAW

Hukumomin Turkiyya Sun Cafke 'Yan Jarida bisa Zana 'Hoton' Annabi Muhammad SAW

  • Hukumomi a kasar Turkiyya sun ce ba za a lamunci rashin kunyar zana hoton Annabi Muhammad Sallahu Alaihi wa Sallam ba
  • Tuni aka kama AnDogan Pehlevan da wasu mutane a Turkiyya bisa zargin zana hoton barkwanci da ya shafi Annabawan Allah Subhanu wa Ta'ala
  • Mujallar da ta buga hotunan, ta nuna wasu mutane biyu a sararin samaniya suna gaisawa, inda daya ya ce sunana Muhammad, dayan kuma Musa

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Kasar Turkiyya – An kama wasu masu zane uku a kasar Turkiyya ranar Litinin bisa zanen barkwanci da aka wallafa a mujallar mako-mako ta Leman.

Mutane da dama sun fassara wani zane da ya nuna Annabawan Allah Subhanahu wa Ta'ala guda biyu; Annabi Muhammad Sallalahu Alaihi wa Sallam da Musa A.S.

Shugaban kasar Turkiyya, Erdogan
Kasar Turkiyya ta kama masu zana Annabawan Allah Subhanahu wa Ta'ala Hoto: Getty
Asali: Getty Images

Reuters ta wallafa cewa an nuna zanen biyu na gaisawa a sararin samaniya, yayin da makamai ke tashi a kasa tamkar cikin gwabza mummunan yaƙi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Turkiyya ta kama Pehlevan da wasu mutum biyu

Ministan harkokin cikin gida na Turkiyya, Ali Yerlikaya, ya wallafa wani bidiyo shafin X, inda aka ga jami’an ‘yan sanda suna kama ɗaya daga cikin masu zanen, Dogan Pehlevan.

A cikin rubutunsa, Yerlikaya ya ce:

"Na sake la’antar wadanda ke kokarin haddasa fitina ta hanyar zana barkwanci game da Annabinmu Muhammad Sallalahu Alaihi wa Sallam."
"Wanda ya zana wannan hoto marar kunya, D.P., ya shiga hannun hukuma. Wadannan mutane marasa kunya za su fuskanci hukunci a gaban doka."

Gwamnatin Turkiyya ta fusata

Yerlikaya daga baya ya kara wallafa wasu bidiyoyi biyu, inda aka ga jami'an tsaro sun cafke sauran mutanen biyu da ke da hannu da zane da wallafa hoton.

Ministan Shari’a na Turkiyya, Yilmaz Tunç, ya tabbatar da cewa an fara bincike a karkashin Sashe na 216 na dokar laifuffuka ta kasar.

Mahukunta a Turkiyya sun fusata
Mujallar Leman ta yi bayani kan zana hoton Annabawa Hoto: Getty
Asali: Getty Images

Zuwa yanzu, ya bayyana cewa an bayar da umarnin tsare mutane shida a kan lamarin, yayin da ake zurfafa bincike domin yanke hukunci a nan gaba kadan.

A wata sanarwa da ta fitar, mujallar Leman ta nemi afuwar masu karatu da suka ji ba dadi saboda zanen tana mai cewa zanen ba wani cin mutunci ga addinin Musulunci ba ne.

Mujallar ta ce:

"Sunan Muhammad daya ne daga cikin sunaye mafi yawan amfani a duniya a matsayin girmamawa ga Annabi Sallalahu Alaihi wa Sallam . Wannan zane ba shi ne yake wakiltar Annabi Muhammad ba, kuma ba a zana shi domin cin mutuncin addini ba."

Turkiyya ta gimtse alaka da Isra'ila

A wani labarin, mun wallafa cewa Shugaban kasar Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan, ya sanar da dakatar da duk wata hulɗar kasuwanci tsakanin kasarsa da Isra’ila yayin da ake yaki da Gaza.

A cewar wata sanarwa da Ma’aikatar Kasuwanci ta Turkiyya ta fitar, an ce matakin ya shafi dukkan nau’o’in cinikayya da kayayyaki – wato har da shigo da kaya da fitar da su daga Isra’ila.

Kasar Turkiyya ta yanke wannan shawara ne bisa la’akari da yadda Isra’ila ke ci gaba da kai hare-hare a Zirin Gaza, tun daga watan Oktoba 2023, inda dubban Falasɗinawa suka rasa rayukansu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.