Mutum 48,000 Suka Rasa Ransu a Girgizar Ƙasar Turkiyya, Recep Erdogan

Mutum 48,000 Suka Rasa Ransu a Girgizar Ƙasar Turkiyya, Recep Erdogan

  • Adadin yawan mutanen da suka rasu a girgizar ƙasar da ta auku a ƙasar Turkiyya ya bayyana
  • Shugaban ƙasar Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan shine ya sanar adadin yawan mutanen da suka rasu a girgizar ƙasar
  • A cewar shugaban ƙasar mutum dubu arba'in da takwas ne suka rigamu gidan gaskiya, yayin da wasu da dama suka jikkata

Ƙasar Turkiyya- Shugaban ƙasar Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan, ya bayyana adadin yawan mutanen da iftila'in girgizar ƙasar da ta auku a kwanakin baya ya halaka a ƙasar.

Shugaban ƙasar ya bayyana adadin yawan mutanen da suka rasa ransu da waɗanda suka samu raunika a ranar Lahadi. Rahoton Punch

Erdogan
Mutum 48,000 Suka Rasa Ransu a Girgizar Ƙasar Turkiyya, Recep Erdogan Hoto: Punch
Asali: UGC

Recep Tayyip Erdogan, ya bayyana cewa mutanen da suka rasu a dalilin girgizar ƙasar su mutum dubu arba'in da takwas (48,000), yayin da sama da mutum dubu ɗari da goma sha biyar (115,000) suka samu raunika, a girgizar ƙasar ta yankin Kudu maso Gabas na ƙasar.

Kara karanta wannan

Kamfen APC Yabar Baya da Ƙura, Ƴan Jagaliya Sun Harbi Tawagar Ɗan Takarar Gwamna, Air Marshal

Shugaban ya bayyana hakan ne a wani jawabi da yayi a gidan talabijin ga ƴan ƙasar daga yankin Samandag na gundumar Hatay.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Adadin yawan mutanen da suka rasu ya kai mutum dubu arba'in da takwas (48,000) sannan yawan mutanen da suka samu raunika ya wuce mutum dubu ɗari da goma sha biyar (115,000). Inji shi

Idan za a iya tunawa dai a ranar 6 ga watan Fabrairun 2023, girgizar ƙasa kashi biyu mai ƙarfin ɗigo 7.7 da 7.6 ta auku a yankin Kudu maso Gabas na ƙasar Turkiyya, an samu tazarar sa'o'i tara a tsakanin su.

An ji motsin ƙasa a gundumomi goma sha ɗaya na ƙasar, tare da ƙasashe masu makwabtaka da ƙasar, inda ƙasar Syria itace wacce abin yafi shafa. Rahoton Vanguard

Saudi Arabiya ta Cafke ‘Yan Najeriya 800, An Yi Bayanin Laifuffukan da Suka Aikata

Kara karanta wannan

"Ku yafe min dan Allah": Inji Direban Motan da Yayi Kicibis da Jirgin Ƙasa a Lagos Mutum 6 Suka Mutu

A wani labarin na daban kuma, ƙasar Saudiyya ta cafke ƴan Najeriya da dama a ƙasar kan aikata laifuka da dama da suka saɓawa dokar ƙasar.

Hukumomin ƙasar Saudiyya sune dai suka yi caraf da ƴan Najeriyar da suka aikata waɗannan laifukan a ƙasar da suka saɓawa doka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel