'Sharuɗan Ganduje ne': APC Ta Fadi abin da Ya Haka Gwamnan PDP Sauya Sheka

'Sharuɗan Ganduje ne': APC Ta Fadi abin da Ya Haka Gwamnan PDP Sauya Sheka

  • Jam’iyyar APC ta zargi Gwamna Ademola Adeleke da yunkurin sauya sheka daga PDP, amma ya kasa cika sharudan da shugabannin APC suka gindaya masa
  • Gwamnan Osun ta bakin mai magana da yawunsa ya karyata zargin, yana cewa bai taɓa tunanin ficewa daga PDP ba ko a baya ko yanzu
  • Gwamnatin Adeleke ta ce APC na ƙirƙirar labarai don ɓoye matsalolinta, yayin da jama'a ke nuna goyon baya ga Adeleke da ayyukansa

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Osogbo, Osun - Jam’iyyar APC reshen jihar Osun ta caccaki Gwamna Ademola Adeleke kan sauya sheka.

APC ta ce gwamna Ademola Adeleke ya nemi sauya sheka zuwa jam’iyyar amma ya kasa cika wasu sharuda.

APC ta kalubalanci gwamna kan komawa jam'iyyar daga PDP
APC ta tona asirin dalilin kin komawar gwamna Adeleke jam'iyyar. Hoto: Gov. Ademola Adeleke.
Asali: Twitter

APC ta tonawa Gwamna Adeleke asiri

Jam’iyyar ta nemi a janye maganar da gwamnan ya yi a taron PDP a Osogbo inda ya ce bai da niyyar barin jam’iyyarsa, cewar Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A baya, APC ta fitar da jawabi da Kola Olabisi ya sa wa hannu, inda ta ce Adeleke ya musanta sauya sheka a wani taron PDP.

Adeleke ya kira jita-jitar sauya shekar da “labarin ƙarya daga masu tsoron nasarorinsa” a jagorancin jihar.

APC ta ce:

“Muna mamakin dalilin da ya sa Adeleke bai faɗa wa tsofaffin jiga-jigan PDP gaskiya kan yunkurinsa na sauya sheka ba.”
APC ta musanta ikirarin gwamna kan sauya sheka
APC a Osun ta tona asirin abin da ya hana Adeleke barin PDP. Hoto: Dr. Abdullahi Umar Ganduje, Gov. Ademola Adeleke.
Asali: Facebook

APC ta yi tone-tone kan Adeleke

Jam’iyyar ta kwatanta lamarin da matar aure mai yawan zuba ido waje tana tunanin sirrinta bai bayyana ba.

APC ta ce mutane sun san yadda wasu gwamnoni da attajirai ke shirya sauya shekar Adeleke da daddare, ciki har da ziyararsa ga Bisi Akande.

Ta ce Adeleke bai bayyana wa jiga-jigan PDP sharudan da APC ta gindaya masa ba, ciki har da rashin tikitin kai tsaye.

Martanin Gwamna kan shirin komawa APC

Sai dai mai magana da yawun gwamnan, Olawale Rasheed, ya musanta zargin, yana mai cewa Adeleke bai taɓa yin yunkurin sauya sheka ba.

Olawale ya ce bayan kayar da mai ci a 2022, Adeleke ya ci gaba da samar da ci gaba da kuma samun yabo daga gida da waje.

Ya ce:

“Da irin wannan tarihin aiki, babu buƙatar Adeleke ya sauya sheka domin samun nasara a 2026.”

Ya ƙara da cewa Gwamna Adeleke bai halarci wata ganawa kan sauya sheka ba, kuma hakan bai taɓa kasancewa cikin shawarwarinsa ba.

A cewarsa, gwamnansa ya fi nasarar APC cikin shekaru uku fiye da abin da jam’iyyar ta yi a shekara 12.

An ba Gwamna shawara kan komawa APC

Mun ba ku labarin cewa kungiyar 'Osun Leaders of Thought' ta bukaci Gwamna Ademola Adeleke da ka da ya bar PDP duk da matsin lamba daga wasu bangarori.

Kungiyar ta shawarci Adeleke ya marawa shugaba Bola Tinubu baya a zaben 2027, saboda dangantakar jin kai da ke tsakanin Osun da shugaban kasa.

Ta ce komawa APC za ta haifar da rikici a siyasar Osun, kuma hakan zai kawo cikas ga mulkin Tinubu da Adeleke.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.