Allah Mai Iko: Dattijuwa Ƴar Shekara 102 Ta Karbi Musulunci, An Yaba da Jajircewarta
- Wani bidiyo mai taba zuciya ya karade intanet, ya nuna wata mata 'yar shekara 104 da ta karɓi Musulunci tana da shekaru 102
- A cikin rahoton, wani mutum ya bayyana cewa matar an haife ta a 1940, kuma yana da katin shaidar ta domin tabbatar da hakan
- Duk da shekarunta, tana zuwa masallaci kullum daga safe har yamma, ta fi jin daɗin salla da jama'a fiye da yin ta ita kaɗai
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kigali, Rwanda - Wata mata mai shekara 104 a duniya da ta karɓi Musulunci a lokacin ta na 'yar shekara 102.
Rahoton ya bazu a kafafen sada zumunta wanda ya nuna dattijuwar bayan ta karbi addinin Musulunci duk da shekarunta.

Asali: Facebook
Wannan na cikin wata sanarwa da shafin Karatuttukan Malaman Musulunci ya yada a jiya Juma'a 2 ga watan Mayun 2025 a shafin Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Fatima ta karbi Musulunci a Kaduna
Mun kawo muku labarin yadda wata mata mai suna Fatima ta Musulunta a Kaduna, inda Sheikh Musa Yusuf Assadussunnah ya ba ta kalmar shahada.
Malamin ya karbi matashiyar ne yayin karatunsa da ya saba yi a masallaci da ke birnin Kaduna a Arewacin Najeriya.
Malamin ya ja hankalinta kan bin tafarkin Musulunci da aikata ibada bisa Sunnah, tare da yin hakuri idan ta hadu da marasa kyawawan halaye.
Sheikh Assadus Sunnah ya yi mata addu'a Allah ya tabbatar da ita kan tafarkin addini, tare da yi mata fatan alheri a sabon matakin rayuwarta.

Asali: Facebook
Dattijuwar yar shekara 102 ta Musulunta
Shafin ya dauko sakon ne daga Daga Malamanmu wanda ke dauke da yadda matar da karbi Musulunci a Rwanda.
Wani mutum mai suna Adnan Rashid ya bayyana yadda dattijuwar ta karbi Musulunci duk da yawan shekarunta.
Mutumin wanda dattijuwar ta karbi Musulunci a hannunsa ya wallafa faifan bidiyo a Facebook domin tabbatar da labarin.
Mutumin ya ce:
“Assalamu Alaikum kowa, ina tare da 'yar’uwarmu dattijuwa, shekarunta 104, an haife ta 1940.
"Ina da katinta yanzu don tabbatar da hakan, ta karɓi Musulunci shekaru biyu da suka gabata tana da 102.”
Mutane sun yaba da jajircewar dattijuwar
Mutumin ya ƙara da cewa duk da tsufanta, tana san muhimman abubuwan Musulunci kuma tana zuwa masallaci kowace rana.
Ya kara da cewa tana zuwa sallah daga safe har yamma, saboda tsufa, tana yin salla da jama’a.
Jajircewarta wajen addini duk da shekarunta ya burge dubban mutane a intanet, mutane sun yaba da tawalinta da yadda take zaman lafiya cikin Musulunci.
Daukacin mutane sun yaba da jajircewarta wnada ke tunatar da cewa shiriya na iya zuwa a kowane lokaci cikin rayuwa.
Matashiya ta karbi addinin Musulunci
A baya, kun ji cewa addinin Musulunci ya samu karuwar wata budurwa yar shekaru 18, wacce ta bar addininta na Kiristanci zuwa Musulunci.
Rahotanni sun tabbatar da cewa kyakkyawar budurwa mai suna Blessing ta sauya sunanta inda ta koma 'Khadijah' a yanzu.
An wallafa hotunan matashiyar wanda ke nunata a lokacin da take Kirista sanye da riga da wando da kuma wanda ta dauka bayan ta zama Khadijah sanye da hijabi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng