Kimiya ta bayyana hanyoyin 3 da iya kawo karshen duniya

Kimiya ta bayyana hanyoyin 3 da iya kawo karshen duniya

Kimiya ta tabbatar da wasu abubuwa 3 da iya sama sanadiyar kawo karshen duniya a nan gaba.

Kimiya ta bayyana
Nukiliya

Cin nasarar Donald trump a matsayin shugaban kasar Amurka ya kara jadada tsoron a zukatun al’umma cewa duniya na iya samin kanta cikin wata babban yakin duniya.

A wata zaben bayar da shawarar da aka gudanar a baya, zaben ta nuna cewa sabon shugaban kasar Amuurka Donal Trump ya gaji mafi yawar kayan fada ta nukiliya, mutane na fargaba cewa zai iya tada wata zauna tsaye wanda ke iya jawo yin amfani da wadanna nukiliya.

Duk da haka, ba ita wannan kawai ne barazana da duniya ke fuskanta a wannan lokacin ba, a cewar jami’ar Oxford gaskiya 'yan adam na fuskantar barazana abubuwa 3 wada zai iya hallaka al’umman duniya gabadaya a yanzu.

Jaridar Metro UK ta rahoto cewa babban hadarin 3 da dan Adam ke fuskanta sune cututtukan annoba, matsanancin canjin sauyin yanayi da kuma yaki da makaman nukiliya. Sabili da aka akwai bukatar shuganin duniya su tashi tsaye akan wannan al’amari.

Matsanin jami’ar Oxford ya bayyana a lokacin da yake jawabi ga masana a fage, ya yi gargadi akan yin amfani da makaman nukiliya.

Y a ce: “Cuta, sauyin yanayi da kuma makaman nukiliya ba zata girmama wa iyakokin wata kasa ba.”

Ku kasance tare da mu@ https://www.facebook.com/naijcomhausa

http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel