Isra’ila Ta Yi Barazanar Yanke Wuta, Ruwa Zuwa Gaza Idan Ba Su Sake Musu ’Yan Uwa Ba

Isra’ila Ta Yi Barazanar Yanke Wuta, Ruwa Zuwa Gaza Idan Ba Su Sake Musu ’Yan Uwa Ba

  • Yayin da ake ci gaba da gwabza kazamin yaki tsakanin Isra’ila da Hamas, Gaza na cikin barazanar rasa ruwa da wutar lantarki
  • Ministan makamashi na Isra’il, Israel Katz shi ya bayyana haka a yau Alhamis 12 ga watan Oktoba inda ya ce daukar matakin ya zama dole
  • Katz ya ce za su yanke ruwa da man fetur da kuma wutar lantarki da su ke samarwa Gaza idan ba su sake musu ‘yan uwa ba.

Gaza, Falasdinu - Ministan Makamashi a Isra’ila, Israel Katz ya sha alwashin dakile taimakon da su ke kai wa Gaza idan ba a sake musu ‘yan uwa ba.

Katz ya bayyana haka ne a yau Alhamis inda ya ce duk wata hanyar taimako za su datse ta wanda su ke taimakon Gaza da su, cewar AlJazeera.

Kara karanta wannan

Isra'ila v Falasdinu: Shahararren Malamin Addini Ya Bayyana Matsayarsu Akan Wannan Rikici, Ya Tura Sako

Isra'ila za ta datse wuta, ruwa da man fetur zuwa Gaza
Isra’ila Ta Yi Barazanar Yanke Wuta, Ruwa Zuwa Gaza. Hoto: BBC.
Asali: Depositphotos

Meye Isra'ila ke cewa kan Gaza?

A ranar Asabar ce 7 ga watan Oktoba, kungiyar Hamas ta kai wani mummunan hari Isra’ila wanda ya yi ajalin mutane da dama, cewar Channels TV.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A martaninta, Isra’ila ta kai farmakin ramuwar gayya inda akalla Falasdinawa 198 su ka rasa rayukansu dalilin harin.

Har ila yau, kungiyar Hamas ta ci gaba da rike Isra’ilawa da dama saboda irin hare-haren da Isra’ila ke musu.

Ministan a martaninsa ya ce:

“Taimakon jin kai zuwa Gaza? babu makunnin wuta da zai yi aiki, babu ruwan fanfo da zai yi aiki.”

Ya kara da cewa:

“Babu wata babbar mota da ke dauke da man fetur da za ta shiga Gaza har sai idan sun sake mana mutanen mu da ke hannunsu.”

Mutane nawa aka kashe a fadan Isra'ila da Gaza?

Kara karanta wannan

Babban Hafsan Tsaron Najeriya Ya Dira Jihar Arewa, Ya Aike da Kakkausan Saƙo Ga Yan Ta'adda, Ya Ba Su Zaɓi 2

Akalla mutane fie da 150 na hannun ‘yan kungiyar Hamas bayan harin ranar Asabar da ya hallaka mutane fiye da 1,200 a yankin.

A kwanakin nan, Isra’ila ta bayyana cewa za ta mamaye Gaza tare da hana su ruwa da man fetur da kuma wutar lantarki.

Kamfanin samar da wutar lantarki na Falasdinu ta bar aiki a ranar Laraba 11 ga watan Oktoba bayan man fetur da su ke samu ya tsaya cak.

Isra'ila ta yi alkawarin kare 'yan Najeriya

A wani labarin, Isra'ila ta yi alkawarin kare 'yan Najeriya da ke zaune a kasar yayin da ake ci gaba da rikici.

Jakadan Isra'ila a kasar Najeriya, Michael Freeman shi ya bayyana haka inda ya ce komai na iya faruwa akasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel