Tashin Hankali Yayin da Jirgin Sama Ya Gamu da Hatsari Bayan Ya Sauka a Legas

Tashin Hankali Yayin da Jirgin Sama Ya Gamu da Hatsari Bayan Ya Sauka a Legas

  • Wani jirgin sama da ya taso daga Owerri, jihar Imo ya gamu da matsala yayin sauka a filin jirgin saman Murtala Muhammad da ke Legas
  • Bayanai sun nuna jirgin ya wuce iyakar titin 18L yayin sauka lokacin ana ruwan sama mai ƙarfi ranar Jumu'a
  • Har yanzu mahukunta ba su ce komai ba amma wata majiya ta bayyana cewa ba bu wanda ya rasa rayuwarsa

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Lagos - Wani jirgin saman fasinjoji na kamfanin United Nigeria Airlines ya sauka daga titin tashi da saukar jiragen sama a filin jirgin Murtala Muhammed (NMA) jihar Legas.

Jaridar Daily Trust jirgin ya samu matsalar da ta kai ga sauka daga asalin titinsa na tashi ko sauka, lamarin da ya haifar da firgici da tashin hankali tsakanin Fasinjoji.

Jirgin sama ya sauka daga titinsa a NMA.
Tashin Hankali Yayin da Jirgin Sama Ya Gamu da Hatsari Bayan Ya Sauka a Legas Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Punch ta ce haɗarin ya faru ne da misalin ƙarfe 7:35 na daren ranar Jumu'a, 8 ga watan Satumba, 2023 a filin jirgin saman NMA yayin da ake zabga ruwan sama.

Kara karanta wannan

Hawaye Sun Kwaranya Yayin Da Matashi Ya Farmaki Malamin Addinini Tare Da Ajalinsa Da Adda, An Bazama Nemanshi

Rahotanni sun bayyana cewa tuni aka fara aikin ceto jim kaɗan bayan jami'an kwana-kwana na filin jirgi (ARFFS) sun isa wurin da lamarin ya faru.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Har kawo yanzu ba bu wani cikakken bayani kan abinda ya faru da jirgin saman amma tuni jami'an ba da agajin gaggawa suka ci gaba da aikin kwashe fasinjoji daga cikin jirgin.

Yadda lamarin ya faru

Wata majiya a filin sauka da tashin jiragen na Murtala Muhammad ta bayyana cewa Jirgin ya dawo ne daga Owerri, babban birnin jihar Imo sa'ilin da matsalar ta auku.

A cewar majiyar, yayin sauka Jirgin ya ci gaba da tafiya har a wuce iyakar titin sauka na 18L da tsawon mita 200, inda ta ƙara da cewa, "Ba bu wanda ya mutu a halin yanzu."

Har kawo yanzu da muka haɗa wannan rahoton, ba bu wata sanarwa a hukumance daga hukumar filin jirgin ko kamfanin jirgin da lamarin ya shafa.

Kara karanta wannan

Tinubu: Gwamnan PDP Ya Manna Hotonsa a Jikin Buhunan Shinkafa, Ya Faɗi Dalili

Jirgin Saman Sojojin Najeriya Ya Yi Hatsari A Jihar Neja

A wani labarin na daban Wani jirgin sojin sama mai saukar angulu mai lamba MI-171 ya yi hatsari a lokacin da yake aikin jigilar mutane zuwa jihar Kaduna daga Neja.

A wata sanarwa da kakakin rundunar sojin sama Edward Gabkwet ya fitar, an bayyana cewa jirgin ya yi hatsari ne jim kaɗan bayan tashinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262