'Sojojin Nijar Sun Yi Garkuwa Da Jakadan Faransa', Emmanuel Macron

'Sojojin Nijar Sun Yi Garkuwa Da Jakadan Faransa', Emmanuel Macron

  • Shugaban kasar Faransa, Emmanuel Macron ya ce sojin Jamhuriyar Nijar su na rike da jakadansu a kasar
  • Macron ya ce yanzu haka yana ofishin jakadancin Faransa da ke Nijar inda sojin ne su ke ba shi abinci
  • Wannan na zuwa ne bayan sojin Jamhuriyar Nijar sun bukaci jakadan Faransa ya fice daga kasar dama sojojinsu

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Paris, Faransa - Shugaban kasar Faransa, Emmanuel Macron ya bayyana cewa sojojin Nijar sun yi garkuwa da jakadan Faransa a kasar.

Macron ya ce sojin sun ajiye jakadan ne a ofishin jakadancinsu da ke Nijar inda ya zargi sojojin da hana duk hanyar kai kayan abinci ga ofishin jakadancin kasar.

Faransa na zargin Sojin sun yi garkuwa da jakadanta a Nijar
Emmanuel Macron na zargin sojin Nijar da garkuwa da jakadanta. Hoto: Emmanuel Macron, Abdourahamane Tchiani.
Asali: Facebook

Meye Macron ke zargin sojin Nijar da yi?

Shugaban ya bayyana haka ne a yau Juma'a 15 ga watan Satumba, TRT Afirka ta tattaro.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya ce yanzu haka jakadan kasar na karbar iya abincin da sojojin su ke ba shi tun da sun hana kai abinci zuwa ofishin.

Ya ce:

"A yanzu haka, akwai jakadanmu da kuma jami'in diflomasiyya da su ke tsare a ofishin jakadancinmu da ke Nijar.
"Sojin sun hana a kai kayan abinci wanda a iya abincin da su ka ba shi yake ci."

Meye sojin su ka ce kan jakadan Faransa?

Sojin Jamhuriyar Nijar sun bukaci jakadan Faransa, Sylvain Itte ya tattara ya fice da ga kasar cikin gaggawa bayan hambarar da Mohamed Bazoum a karshen watan Yuli.

Amma Faransa ta ki amincewa da haka saboda ba ta amince da gwamnatin sojin ba inda ta ke ganinta a matsayin haramtacciyar gwamnati, cewar Al-Jazeera.

Kasar Faransa na da sojoji kusan dubu daya da dari biyar a Jamhuriyar Nijar inda sojin kasar su ka umarcesu da ficewa a kasar tun farkon watannan da mu ke ciki.

Faransa Na Rokon Morocco Kan Kin Karbar Tallafi Na Girgizar Kasa

A wani labarin, Yayin da kasar Morocco ke cikin wani hali bayan girgizar kasa, kasashe da dama na ba da na su gudumawa.

Kasar Faransa ma ba a barta a baya ba, ta yi kokarin kawo tallafi, amma kasar Morocco ta ki amincewa.

Wannan ne ya saka gwamnatin Faransa rokon Morocco da ta daure ta karbi wannan tallafi da ta ke kokarin bata yayin da aka rasa rayuka da dama.

Asali: Legit.ng

Online view pixel