Wani dan kasar Morocco ya zo Nigeria a kan Keke don yawon bude ido
- Rahotonanni sun bayyana cewa wani mutumi ya yi doguwar tafiya a kan Keke
- An ce mutumin ya zo Nigeria tun daga kasar Morocco a saman Keke
- Ya bayyana cewa ba wannan bane karon sa na farko da ya fara yin tafiya mai nisa a saman Keke
Legit.ng ta ci karo da wani labari na wani mutumi mai abun al'ajibi, wanda ya yi doguwar tafiya daga kasar Morocco zuwa Nigeria a saman Keke. An fara daukar hotunan mutumin mai suna Yasinu Riskalai a lokacin da ya isa Saminaka, inda jama'a suka taru don jin wannan abun al'ajabi daga bakinsa.
Wani dan Nigeria mai suna Sani Musa Saminaka ne ya aika da wannan labarin al'ajabin a lokacin da ya hadu da mutumin a jihar Saminaka.
A cewar Saminaka, Yasinu Riskalai ya yanke shawarar zuwa Nigeria daga Morocco a akan Keke don yawon bude ido, da kuma kai ziyara manyan wuraren da ya dade yana jin labarinsu. Mutumin ya ce yana son ya dauki hotunan wuraren da ya ziyarta don zama tarihi a gare shi.
KARANTA WANNAN: Akalla mutane 2,700 ne suka sauya sheka daga APC zuwa PDP a birnin tarayya Abuja
Saminaka ya kuma bayyana cewa Yasinu Riskalai ya shaida masa cewa shi Musulmi ne, haka zalika a yawace yawacensa zai leka babban birnin tarayya Abuja don ganewa idanuwansa abubuwan ban mamaki.
Sani Musa Saminaka wanda ya dora wannan labarin a shafinsa na Facebook, ya kara bayyana cewa ya hadu da Yasinu Riskalai ne a Saminaka, jihar Kaduna, inda ya ce ya ci karo da mutumin ne yana daukar hotuna da mutanen garin da suka nuna sha'awarsu akan labarin tafiye tafiyensa na ban al'ajabi.
Karnata labarin a kasa:
KARANTA WANNAN: Wata babbar kotun Ikeja ta yankewa wasu yan ta'adda 2 hukuncin shekaru 42 a gidan wakafi
A baya ma Legit.ng ta ruwaito cewa wata mata yar kasar China ta zo Nigeria daga kasar Morocco a kan Keke. Matar an bayyana sunanta da Huang Shuang wacce ta bayyana sha'awarta na zagaya duniya a kan Keke.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Matar da ta haifi yara 5 a lokaci daya a garin Awuka | NAIJ TV
Asali: Legit.ng